Kotun ICC ta fara shari'ar shugabannin siyasar Kenya
September 12, 2013Talla
Waɗanda ake tuhumar dai, ana yi musu shari'a ne bisa rikicin da ya biyo bayan zaɓen ƙasar Kenya a shekara ta 2007, inda rikicin ya yi sanadiyar mutuwar muta ne kimanin 1200, kana wasu sama da dubu biyar suka rasa ma tsugunensu. Wannan shari'ar dai ta ɗauki hankalin ƙasashen duniya, inda masu kare 'yancin ɗan Adam ke ganin shari'ar wani saƙo ne ga shugabannin da ke son yin amfani da muƙamansu don take 'yancin talakawa. To amma fa shari'ar tana fiskantar suka daga ciki da wajen ƙasar ta Kenya, musamman 'yan ƙasashen Afirka da ke kallon kotun mai hukunta man'yan laifuka ta ICC, ta fi mayar da hankali ne kan laifukan da 'yan ƙasashen Afirka ke aiktawa, yayinda a gefe guda suke yin biris da ta'asar da wasu manyan ƙasashen duniya ke aikatawa.