Ruto ya ƙi amsa zargin ingiza rikici a Kenya
September 10, 2013Mataimakin shugaban ƙasar Kenya William Ruto ya ƙi amsa zargin da ake masa na tafka manyan laifukan yaƙi a shari'ar da yake fuskanta a Kotun hukunta miyagun laifukan yaƙin na ICC dake birnin La Hague. Wannan shari'a dai na janyo fargaba a zukatan mutanen Kenya da ke gida, waɗanda ke ganin mai yiwuwa shariar ta sake tayar da rikicin siyasa makamancin wanda ya afku a shekarar 2007.
Babbar mai shigar da ƙara a kotun na ICC ke nan Fatou Bensouda take cewa: "Masu shari'a, hujjojin da masu shigar da ƙara zasu gabatar, zasu tabbatar muku da cewa laifukan da ake zargin Mr Ruto da Mr Sang da aikatawa, ba wai an tabka sune haka nan ba, a 'a an ɗauki lokaci ne aka shirya aka aiwatar da shi da burin ƙuntatawa magoya bayan jami'yyar PNU"
William Ruto da Joshua Sang wanda ake tuhumarsu tare na fiskantar zargin haddasa tashe-tashen hankula, bayan zaɓe shekaru biyar da suka wuce, inda suka haɗa baki da wasu su kashe mutane da dama, suka kuma tasa ƙeyar magoya bayan jami'yyun da ke hammaya da su a ƙasar Kenya.
Hujjojin mai shigar da ƙara
A jawabin buɗe shari'ar da ta yi mai shigar da ƙara a Kotun na ICC Fatou Bensouda, ta haƙiƙance cewa a cigaba da shari'ar, kuma ta yi gargadin cewa an tsorata wasu shaidu an kuma bai wa wasu cin hanci
Babban burin Mr Ruto shi ne ƙwatar iko wa kansa da jamiyyarsa, ta yin amfani da ƙarfin tuwo, kuma hakan ya kasance ne saboda ya gaza yin haka ta hanyar samun kuri'un jama'a
Wannan ne karon farko da wani babban ɗan siyasan da ke mulki zai kasance a kotu domin fiskantar shari'a ta ƙasa da ƙasa, ana ma sa ran cewa shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta abokin hammayar William Ruto a baya wanda kuma shi ne mataimakinsa yanzu shi ma zai gurfana a gaban kotun domin amsa zargi makamancin na Ruton daga farkon watan Nuwamba idan Allah ya kai mu. Kotun dai ya cika maƙil da 'yan majalisan Kenya da iyalan William Ruto waɗanda suka kwashi jiki suka bi shi har kotun dan nuna masa goyon baya.
Gardamar masu kare William Ruto
Sai dai Kharin Khan Lauyan William Ruto ya ce wata rana zaa ƙaddamar da binciken da zai duba dalilin da ya sa aka ɗorawa Ruto wannan laifin babu gaira babu dalili saboda ko a yanzu akwai ƙarancin shaidu a shari'ar
Ya yi kamar mutane da yawa na da burin samun hujjoji ko ta halin ƙaƙa, ko da ma basu dace ba, domin kawai a sami Ruto da laifi, kuma idan aka yi la'akari da abin da ɓangaren masu shigar da ƙaran ke gabatarwa, ya kamata a yi la'akari da cewa shaidu daga shiddan da babban mai shigar da ƙara Luis Moreno Ocampo ya gabatar ranar 15 ga watan Disemban shekarar 2010, uku daga cikinsu sun riga sun faɗi
Wannan shari'a dai ya raba ra'ayoyin mutane gida biyu da waɗanda ke cewa hujjojin da za a bayar a kotu ka iya tayar da ɓacin ran da aka kama hanyar mantawa da shi, da kuma waɗanda ke cewa wannan shari'a na zaman zakarar gwajin dafi na Kotun na ICC wanda har yanzu ya gaza yin nasara a sharioinsu kuma take fuskantar zargin cewa ta fi mayar da hankali kan ƙasashen Afirka a maimaikon sauran ƙasashen duniya.
Ƙorafin waɗanda abin da shafa
Lauyan da ke wakiltar waɗanda abin ya shafa Wilfred Nderitu ya ce an yaye musu mutuncinsu kuma suna cigaba da rayuwa cikin barazana da tsoro..
A dalilin haka ku masu shari'a kuke da alhakin gudanar da aiki mafi wahala, na tabbatar da cewa an gudanar da bincike kan janyewar waɗanda ake zargi da waɗanda abin ya shafa daga shari'ar, ku kuma ɗauki matakan da suka dace, waɗanda nake wakilta na da ra'ayin cewa idan har kuka yi haka, zaku ƙara ƙimar ku a idanunsu, shi sa duk da irin koma bayan da ake samu a wannan shari'a, waɗanda abun ya shafa suke kallonku da kyakyawar fata, na cewa, zaku kamanta adalci a wannan shari'a
Abin jira a gani dai shi ne yadda zata kaya a wannan shari'a kasancewar duk mutane 18 da kotun ta taɓa yankewa hukunci 'yan Afirka ne.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Awal Balarabe