1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenyatta ka iya tsayawa takarar zabe a Kenya

February 15, 2013

Babbar kotun kasar Kenya ta bude hanya ga mataimakin Firaminista Uhuru Kenyata ya fito a fafata da shi a zaben kasar da za a yi a watan Maris mai zuwa.

https://p.dw.com/p/17fD6
epa02623841 (FILE) A file photo dated 15 December 2010 shows Kenya's Finance Minister and Deputy Prime Minister Uhuru Kenyatta arriving at a press conference on the day the International Criminal Court (ICC) announced six prominent Kenyans, which included Kenyatta, who are said to be responsible for masterminding the country's 2007/08 post-election violence that left some 1,300 dead. According to a local report, five suspects, Kenyatta, former higher education minister William Ruto, suspended Industrialisation Minister Henry Kosgey, former police commissioner Maj-Gen Hussein Ali, and Head of Operation at KASS FM radio Joshua Arap Sang said on 09 March 2011 that they will honor summonses issued for the charges of crimes against humanity by the pre-trial chamber of the ICC. The sixth suspect is the Secretary to the Cabinet and Head of the Civil Service Francis Muthaura. EPA/DAI KUROKAWA
Hoto: picture-alliance/dpa

Ya zuwa yanzu dai babbar kotun kasar Kenya ta bude hanya ga mataimakin Firaminista Uhuru Kenyata ya fito a fafata da shi a zaben kasar da za a yi a watan Maris mai zuwa, bayan da babbar kotun kasar ta ce hukumar zabe mai zaman kanta da hukumar yaki da ayyukan almundahna da cin hanci suke da alhakin bayyana dan takara da cewa ya cancanta ya tsaya takara ko akasin haka.

Kenyatta wanda tsohon ministan kudine kuma da ga tsohon shugaban kasa na daya daga cikin mutane hudu da kotun hukunta manyan laifuka ke zargi da iza wutar rikicin kabilanci da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 1,200 sama da dubu dari shida kuma suka kauracewa muhallansu bayan zaben da aka yi a kasar a shekarar 2007. Haka zalika wannan kotu ta wanke abokin karawarsa William Ruto.

Masu fafitikar hakkin bil Adama a wannan kasa sun bukaci ganin cewa kotun bata bar wadannan ´yantakaraba su shiga neman madafun iko, duba da cewa duk wanda zai rike wata kujerar ofis a sabon kundin tsarin mulkin kasar dole ya zama mutum mai cikakkiyar kima da mutane ke mutuntawa .

The eight Kenyan presidential aspirants Mohammed Dida, James Ole Kiyiapi, Uhuru Kenyatta, Peter Kenneth, Musalia Mudavadi, Martha Karua, Kenyan Prime Minister Raila Odinga and Paul Muite (L-R) face off in the first ever presidential debate at Brookhouse School in Kenya's capital Nairobi February 11, 2013. The presidential television debate - the first ever held in the country - failed to produce a clear winner, but gave an early taste of what is expected to be a highly charged contest to run East Africa's economic powerhouse. Picture taken February 11, 2013. REUTERS/Stringer (KENYA - Tags: ELECTIONS POLITICS)
Mahawarar 'yan takarar zaben KenyaHoto: Reuters

Godfred Mosila kwararrene kan harkokin da suka shafi sharia a birninn Nairobi na kasar Kenya.

"Dama hukuncin an tsammaci zai zama haka saboda kimanin shekaru biyu kenan da aka gabatar da shi a gaban kotu aka ki fitar da sakamakonsa, sai a wannan kurarren lokaci duk kuwa da tangarda da ke cikinsa na amince da wani bangare na hukuncin."

Wannan rashin aminta da hukuncin baki daya ya sa masu fafitika sake gabatar da wata sabuwar bukatar a gaban hukumar kare hakkin biladama ta kasar ta Kenya da hukumar masana sharia ta kasa da kasa reshen kasar ta Kenya da cibiyar kasa da kasa kan tsare tsare da rikici.

To ko meye ya sa suka ki amince da wannnan hukunci baki dayansa ananma Mosila ya yi karin haske:

Kenia Wahl 2013: Fünf Richter des Hohen Gerichts, die darüber entscheiden, ob Uhuru Kenyatta und William Ruto als Präsidentschaftskandidaten zugelassen werden. Bild: DW Korrespondent James Shimanyula, Nairobi, Kenia, 15.02.2013
Zaman alkalan babbar kotun da ta wanke 'yan takaraHoto: DW/J. Shimanyula

"Ko da yake na duba abinda ´yanuwana a fannin sharia suka fada inda alkallan ke cewa basu da ikon tsaida dantakara, ba aikinsu bane sai dai wannan ba zai rasa nasababa da ganin irin girman mutanan da ke cikin wannan sharia wato ´yantakarane na shugabancin kasa shi yasa su ka nemi a tura abin gaban kotun koli, amma shashi na shida na sabon kundin tsarin mulkin kasar da ke lura da kimar mutane da zasu rike mikaman gwamnati abune da babbar kotu ke da alhakin fitar da hukuncinsa musamman saboda kusancinsa da zaben shugaban kasa."

Shi dai Kenyata mataimakin Firaminista na da laifuka biyar da kotun ta kasa da kasa ta ICC ke zarginsa a kansu da suka hadar da alaka da kisan jamaa da fyde da sanya mutane kauracewa muhallansu da sauransu

shi kuwa Ruto tana tuhumarsane da laifuka 3.Sai dai dukkansu wannan kotu ta wanke su inda suka yi alkawarin cigaba da bada hadin kansu gareta.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal