1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar mai gabatar da karar Kotun ICC

June 15, 2012

An rantsar da Fatou Bensouda 'yar asalin Gambiya a matsayin mai gabatar da kara ta kotun hukunta manyan laifufuka a ranar juma'a.

https://p.dw.com/p/15Ful
Gambian war crimes lawyer Fatou Bensouda takes the oath to become the new prosecutor of the International Criminal Court (ICC) during a swearing-in ceremony at The Hague in the Netherlands June 15, 2012. Bensounda replaces Luis Moreno-Ocampo of Argentina. REUTERS/Bas Czerwinski/Pool (NETHERLANDS - Tags: CRIME LAW POLITICS)
Fatou BensoudaHoto: Reuters

An rantsar da matar nan 'yar asalin kasar Gambiya Fatou Bensouda a matsayin wadda ta maye gurbin Luis Moreno-Ocampo dan kasar Argentina tsohon mai gabatar da kara na kotun hukunta mayan laifufuka ta ICC a yau juma'a.

Matar dai 'yar shekaru 51 a duniya ta kasance mataimakiyar babban mai gabatar da kara a kotun tun a shekara ta 2004.

A can farko ta taba rike mukamin ministan harakokin shari'a na gambiya kamun daga bisani ta yi iaki a kotun kasa da kasa ta Rwanda wato (TPIR) da ke da cibiyarsa a birnin Arusha na Tanzaniya.

Yanzu haka dai madam Fatou Bensouda nada jan aiki a gabnta inda kotun ke shari'ar manyan laifufuka guda 7 akasarinsui a Afrika da suka hada da Cote d'Ivoire,Jamhuriyar Demokradiyar Kongo da kuma Libiya.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Zainab Mohammed Abubakar