Borno: Sabon hari yayin ziyarar Buhari
December 23, 2021Bayan kaddamar da ayyuka, Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma gana da dakarun sojoji da ke filin daga tare da rakiyar manyan hafsoshin tsaro na Najeriya. Awa guda kafin saukan shugaban na Najeriya, mayakan na ISWAP suka harbor rokoki guda biyar daga bayan garin Maiduguriinda wasu suka fada unguwannin da ke kusa da filin jirgin da shugaba kasa ya sauka.
Wannan dai shi ne na farko da ake samun irin wanann hari a dai-dai lokacin da shugaban kasa ke kawo ziyara a wannan yankin da ziyara ke zama ta byu a cikin wannan shekara a yankin da ke fama da mastalolin tsaro. A dai-dai lokacin da aka harba wadannan rokoki manyan hafsoshin tsaro na Najeriya su na filin jirgin da Shugaba Buhari zai sauka lamarin da ya daure kan jama'a a game da yadda mayakan suka samu zarafin kai hari a wannan lokaci.
Karin Bayani: Najeriya: Karfin sojoji ya kusa kare wa
Babu dai wata masaniya kan manufa ko burin da mayakan ke son cimma da wadan hare-haren, sai dai hare-haren na kara nuna tabarbarewar tsaro a yankin Arewa Maso Gabashin kasar, da kuma irin barazanar da Kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ke yi da ake ganin sun mamaye wurare da dama duk da dai hukumomi da jami’an tsaro na karyatawa.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi jawabi ga al’ummar a jami’ar Maiduguri bai tabo maganar hare-haren da mayakan ISWAP su ka kai ba, sai dai ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta samu makamai da ta za magance duk matsalolin tsaron da kasar nan ke fuskanta.
Karin Bayani: Blinken: Za mu ci gaba da tallafa wa tsaro a Najeriya
Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya kamala ziyarar tare da karfafa gwiwar sojoji da su kara jajircewa don kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da su a kasar inda ya ce, gwamnati za ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an ba su kayan aiki da su ke bukata.
Karin Bayani: Ziyarar shugaban Najeriya a jihar Borno
Wakilinmu na Maidugurin Al-Amin Suleiman Muhammad ya ruwaito cewa wasu bayanai daga cibiyoyin lafiya sun nuna an samu asarar rayuka biyar, wasu da dama kuma su ka jikkata. Rahotanni sun nunar da cewa, mayakan ISWAP ne suka harba rokokin cikin wasu unguwanni Maidugurin.
Unguwannin da aka harba rokokin sun hada da Ajilari Cross da Bumum Kotu, wadanda ba su da nisa da filin jirgin sama na Maidugurin. Ya zuwa yanzu ana jinyar wasu da su ka jikkata daga wannan harin rokoki, inda ake shirin yin jana'izar wadanda su ka riga mu gidan gaskiya.