An gano yadda ISWAP ke samun kudin shiga
December 6, 2021A wani abu da ke nuna irin jan aikin da ke gaban 'yan mulkin Najeriya da ke fatan kai karshen annoba ta ta'addanci a cikin kasar, wani rahoto na kungiyar kasashen yankin yammacin Africa ta ECOWAS ya ce, Kungiyar ISWAP ta iya shigar da kudin da ya kai Naira miliyan dubu 18 cikin tsarin kudin kasar domin harkokinta.
Har ya zuwa yanzun dai ISWAP na rikida irin ta dashi mai rai guda tara. Kuma ko bayan nasarar hadiye abokiyar adawarta ta Boko-Haram kungiyar na shirin wucewa da sanin 'yan mulki a kokari na fadada harkokinta cikin tarrayar Najeriyar. Wani rahoto na kungiyar da ke yakar kudin haramun a kasashen yankin yammacin Africa ta ECOWAS ya ce, mayakan ISWAP na hada-hadar kudin da ta kai Naira Miliyan dubu 18 a shekara cikin kasar.
Karin Bayani: Najeriya ta tabbatar da kisan al-Barnawi
Kudaden kuma da mafi yawansu ke zaman na harajin da suke karba daga noma da sana'ar su a cikin yankin tafkin Chadi. Rahoton ya kara da cewa, masu mulkin tarrayar Najeriya sun gaza hana kungiyar walwalar kudi duk da jeri na matakan da Abujar ke ikirarin dauka. Jami'an tsaron kasar da hukumomin yaki da kudade na haramun a cikin tarrayar Najeriyar, acewar rahoton, sun gaza iya kai karshen matsalar da ta kalli kungiyar nuna alamun karfi duk da kamfen din kare tasiri na kungiyar.
ISWAP ta sauya taku daga kungiyar Boko-Haram na mai da hankali wajen karbe haraji maimakon hari ga mazauna kasashen yankin tafkin Chadi. Batun na haraji na zaman sabon tsari na kungiyar da a baya ta kalli toshe kafofi na kudadenta dama kame da dama a cikin 'yan canjin da ke taimakawa harkokinta. Yawan kudaden na kuma kara fitowa fili da girman tasirin ISWAP din a daukacin yankin tafkin Chadi da ke takama da kiwon kifi da dabbobi.
Karin Bayani: ISWAP ce ta kai wa sojojin Nijar hari
To sai dai kuma ko ya zuwa ina kungiyar take shirin ta kai cikin fatan lallashin, na iya bata damar girma da karbuwar tsakanin al'ummar yankin, ga hukumar kula da kai-kawo na kudade na harmun din tarrayar Najeriyar, rahoton na zaman tsohon yayi da baya tasiri a cikin tafkin Chadi a yanzu a fadar Sani Tukur da ke zaman kakaki na hukumar.
Sama da masu sana'ar canji na kudi kimanin dari hudu ne, har yanzu ke hannu na jami'an tsaron tarrayar Najeriya bisa laifin tura kudi ga mayakan na kungiyar ta'adda, a wani abun da Abujar ke fatan na iya kai karshen samar da kudade ga kungiyar. Kafin sabo na rahoton da ke shirin nuna irin jan aikin da ke tafe kan hanyar warware matsalar da kudi ke tasiri wajen rura wutar.