Blinken: Za mu ci gaba da tallafa wa tsaro a Najeriya
November 18, 2021Sakataren harkokin kasashen ketare na Amirka Antony Blinken ya bayyana cewa sun sanya hannu kan yarjejeniyar shirin tallafin raya kasashe da Tarayyar Najeriya. Blinken ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ganawarasa da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari yayin ziyarar da yake a yanzu haka a wasu kasashen nahiyar Afirka.
A cewarsa dai yarjejeniyar da suka sanya wa hannu tare da ministan harkokin waje na Najeriyar Geoffrey Onyeama za ta lashe zunzurutun kudi har dalar Amirkan biliyan biyu da miliyan 17. Ya kara da cewa Amirka za ta ci gaba da tallafa wa harkar tsaron Najeriyar da ke ci gaba da tabarbarewa.
A cewar mahkuntan Najeriyar dai, Blinken ya kai ziyara Najeriyar da ke zaman kasa mafi yawan al'umma a Afirka ne, domin tattauna batun tsaron cikin gida da kuma na yankin Sahel da ma batun yiwuwar Amirkan ta ba da taimakon da sojoji da bayanan sirri ga Najeriyar, a yakin da take da 'yan ta'adda.