1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta yi ikirarin harbo jirgin soji

April 2, 2021

'Yan ta'adda Boko Haram sun dauki alhakkin kakkabo jirgin sojin Najeriya da ya yi batan dabo kwanaki biyu da suka gabata. Ko a watan Oktoban 2014 ma mayakan na Boko Haram sun harbo wani jrgin saman yakin Najeriya .

https://p.dw.com/p/3rXK9
Nigeria Militärflugzeug stürzt beim Anflug auf den Flughafen Abuja ab
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Kungiyar Boko Haram da ke karkashin jagorancin Abubakar Shekau ta dauki alhakin kakkabo jirgin yakin Sojin Najeriya mai lamba NAF475 wanda hukumomi suka ayyana bacewarsa tun a ranar Laraba. Kungiyar ta sanar da hakan ne a wani sakon bidiyon na tsawon mintuna 7 da rabi da ta fitar, jim kadan bayan rundunar sojin kasar ta ce jirgin faduwa ya yi.

An daina jin duriyar jirgin saman kwanaki biyu da suka gabata, yayin da ya ke shawagi a sararin samaniyar dajin Sambisa dauke da matuka biyu. Mustapha Ibrahim wani masanin tsaro a tarayyar ta Najeriya ya bayyana cewa abun tashin hankali ne in dai har mayakan sun kai fagen kakkabo jirgin yaki.

Ko a watan Oktoban shekara ta 2014 ma mayakan na Boko Haram sun harbo wani jrgin saman yakin Najeriya inda suka nuna yadda suka halaka matukin a wani faifayin bidyo da su ka nuna.