Tigray na fafutukar samun zaman lafiya bayan yaki
November 2, 2023Kafin yakin da aka gwabza tsakanin sojojin kasar Habasha da na kungiyar ‘yan tawayen Tigray (TPLF) shekaru uku da suka gabata, Haftom Kidai dan shekaru 25 da haihuwa ba shi da gogewar aikin soja, bai taba daukar bindiga ba, balantana ma ya san yadda ake harba ta. Amma lokacin da aka fara yakin, sojojin Habasha da na Iriitriya sun shiga yankin Tigray inda suka fara aikata ta'asa, daga nan ne Haftom ya samu horon soja kuma ya shiga yakin kamar yadda sauran matasan Tigray suka yi.
Karin bayani: Rikici ya tilasta 'yan Habasha gudun hijira
Haftom ya samu munanan raunuka a fagen daga. Yanzu rabin jikinsa ya shanye kuma yana zaune a wata cibiyar kula da sojoji a babban birnin Tigray, wato Mekelle. Amma duk da raunikan da ya samu, ba ya yin nadamar yin yakin ba. Haftom Kidai ya ce: "Na shiga gwagwarmayar kasata domin al'ummata, don kaina, ba na yin nadamar sadaukarwar da na yi, na yi abin da ya kamata in yi, amma yanzu dukkanmu a nan har da ni mun zama masu bukata ta musammun. ina da bukatu da yawa, babban abu shi ne ina son a ba ni magani."
‘Yan kasar Habasha da dama sun yi asara mai yawa a lokacin barkewar kazamin yakin da aka fara daga uku ga watan Nuwamban 2020 zuwa uku ga Watan Nuwaban 2022. An kashe akalla mutane dubu 600,000 yayin da wasu da dama suka jikkata, a cewar tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da ya jagoranci shiga tsakani a lokacin rikicin. Bugu da kari, MDD ta yi kiyasin cewa fadan ya raba kusan mutane miliyan 1.7 da muhallansu tare da haddasa illa ta jiki da ta tunani ga miliyoyin 'yan kabilar naTigray. Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ce ta shiga tsakani a birnin Pretoria na Afirka ta Kudu wajen kawo karshen yakin basasar tsakanin sojojin yankin na Tigray da na gwamnatin Habasha a ranar 3 ga Nuwamban 2022.
Karin bayani: An tabbatar da zaman lafiya a Habasha
Hagos Tesfay, wani dan yankin Tigray da ke zaune a gundumar Erob ya ce bayan cimma yarjejeniyar har yanzu da sauran matsaloli, inda ya ce: "Tun lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya al'amura kamar bankuna da al'amuran sadarwa da wutar lantarki, wadanda aka rufe a mafi yawancin yankunan Tigray, an bude su. Amma a Erob, babu abin da ya canza, yawancin yankunan Erob suna cikin hannun sojojin Iritiriya"
Da yawa daga ciki al'ummar yankin na Tigray na ci gaba da neman ganin an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattaba hannu kanta kamar yadda ya kamata. A cewar gwamnatin yankin Tigray, sama da mutane miliyan biyu da yakin ya raba da gidajensu ba su dawo gida ba. Sannan har yanzu akwai sojojin Iritiriya da mayakan Amhara a yankin na Tigray.
Karin bayani: Eritiriya ta aike da sojinta zuwa Tigray
Redaei Halefom, shugaban kula da harkokin sadarwa na yankin na Tigray ya ce: "Muna sa ran gwamnatin tarayya za ta fitar da su baki daya, dukkanin dakarun tsaron Habasha da ke a cikin yankin Tigray kamar yadda yarjejeniyar ta tanada. Haka muna sa ran mayakan Amhara da sojojin Iritiriya za su fice daga yankin na Tigray."
Barkewar fari da cututuka irin su kwalara da zazzabin cizon sauro sun haifar da barna da ta ta'azzara al' amura a yankin Tigray biyo bayan yakin, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD (OCHA),wanda ya ce akwai bukatar agaza wa al ummar yankin.