1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Rikici a yankin Kahon Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 12, 2020

Kasar Habasha da ke yankin Kahon Afirka, na kokarin afkawa cikin rikici da ka iya juyewa zuwa yakin basasa, bayan da firaministan kasar ya zargi 'yan awaren Tigray da kai hari kan sojojin kasar.

https://p.dw.com/p/3lD3d
USA, Washington I Protest gegen Genozid in Tigray
Al'ummar Habasha na son a hana Firaminista Abiy Ahmed aikata kisan kiyashiHoto: Nicholas Kamm/AFP/Getty Images

Shekara guda ke nan dai da Firaminista Abiy Ahmed ya samu nasarar lashe lambar yabo da zaman lafiya ta Nobel. Sai dai kuma a yanzu wani rikici da ya bullo a kasar na nemanya kai shi ya baro, bayan da ya dauki matakin mayar da martani da karfin soja kan wani farmaki da aka kai sansanin sojojin kasar. Abiy Ahmed dai ya dora alhakin harin a kan 'yan awaren Tigray da ke yankin arewacin kasar.

An yi ta fargabar yiwuwar barkewar yakin basasa, sai dai Abiy ya nunar da cewa sojojin kasarsa sun samu gagarumar nasarar a wannan yanki, da rikicin da aka kwashe tsawon mako guda ana fama da shi ya tilastawa dubban mutane kauracewa kasar zuwa makwabciyar kasar Sudan. 

Rahotanni sun nunar da cewa wadannan mutane da suka tsere da mafi yawanasu suka kasance mata da kanan yara, akwai fargabar za su fada cikin matsanancin hali na bukatar taimako da daukin gaggawa.