1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Eritiriya ta aike da sojinta zuwa Tigray

Ahmed Salisu
September 18, 2022

Rahotanni daga Eritiriya na cewar an fara shirin aikewa da dakarun kasar yankin nan na Tigray da ke kasar Habasha a wani mataki na bada tallafi ga makwabciyarta a yakin da ta daura da 'yan awaren Tigray.

https://p.dw.com/p/4H1p0
Eritrea Äthiopien Soldaten Flash-Galerie
Hoto: AP

Wadanda suka shaida lamarin sun ce sojin na Eritriya na cikin damara irin ta yaki, lamarin da ya sanya kasashen Birtaniya da Kanada yin kira ga 'yan kasashensu kan su yi taka-tsantsan.

Shugabannin 'yan awaren yankin na Tigray ma dai sun tabbatar da wannan lamari, inda suka ce sojin shirye suke tsaf su shiga yakin da aka dawo da shi a cikin watan Agustan da ya gabata.

Rikici tsakanin 'yan Tigray da dakarun gwamnatin Habasha ya jawo rasuwar dubban mutane, yayin da ya jefa miliyoyi cikin yanayi na kunci saboda rashin ababen more rayuwa ciki kuwa har da katse sadarwa.