Jamus: An kama hanyar kafa gwamnatin hadaka
January 26, 2018Talla
'Yan jam'iyyar na SPD da dama ba su amince da bude shawarwari wadanda za su kai ga girka kawance siyasar da ake wa lakabi da GROKO, wannan nasara da aka cimma za ta kawo karshen rikita-rikitar siyasar da Jamus ta samu kanta a ciki tun bayan babban zaben kasa na watan Satumban shekara ta 2017.