SPD ta amince da yin gwamnatin hadaka da CDU
January 21, 2018Zaben dai ya kasance da kankane rinjaye na kuri'ar raba gardamar da aka kada a tsakanin ya'yan jami'yyar ta SPD a Bonn domin bude shawawarin kafa gwamnatin hadaka da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel. A cikin wakilai 642 da suka kada kuri'u 362 suka amince da bude shawarwarin na kafa gwamnatin hadakar tsakanin jam'iyyun siyasar na SPD da CDU domin kawo karshen sarkakiyar siyasar da Jamus din ta samu kanta a cikin tun bayan zaben 'yan majalisun dokokin da aka gudanar a cikin watan Satumba da ya gabata, wanda har kawo yanzu babu sabuwar gwamnati. 'Yan jam'iyyar na SPD da dama ne ba su amince da bude shawarwarin ba wadanda za su kai ga girka kawance siyasar da ake wa la'akabi da Groko. Saboda sabannin manufofin da ke a tsakanin jam'iyyun siyasar a kan batun 'yan gudun hijira. Shi da kansa jagoran jam'iyyar ta SPD Martin Schulz wanda jam'iyyarsa ta fadi a zaben watan Stumbar da ya gabata, tun da farko ya yanke shawara dakatar da kawance tsakanin SPD da CDU To amma daga bisanin ya yi ammai ya lashe a game da wasu dalilai da ya bayyana na kaucewa Jamus fadawa cikin matsala ta siyasa ta rashin kafa gwamnati. Abin da ka iya janyo cikas ga kugiyar tarrayar Turai daf da lokacin da ake kokarin kaddamar da sauye-sauye na tattalin arziki a cikin kungiyar.