Kuri'ar nema wa siyasar Jamus mafita
January 21, 2018A wannan Lahadin ce jam'iyyar SPD a nan Jamus ke gudanar da taro domin yanke hukuncin karshe kan kulla kawance da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ko akasin haka. Taron wanda ke gudana a birnin Bonn ya karbi bakuncin 'ya'yan jam'iyyar da sauran masu fada a ji, inda a share guda wadanda ke adawa da yin kawance da CDU suka gudanar da zanga-zanga a gaban dakin taron.
Wakilai 600 na jam'iyyar SPD ne za su kada kuri'ar bayyana matsaya kan tattaunawa a hukumance da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel. Baya ga su wadannan wakilan, akwai ma wasu 'yan jam'iyyar ta adawa SPD su dubu 440 da za su kada kuri'a ranar Lahadi a birnin Bonn.
Jagoran SPD Martin Schulz na fuskantar suka daga wasu daga rassan jam'iyyar musamman matasa, wadanda ke da ra'ayin jam'iyyar ta kafa kanta a matsayinta na mai adawa, saboda kayen da ta sha a zaben watan Satumbar bara.
Wasu jiga-jigan jam'iyyar ta SPD sun tabbatar da samun hadin kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar da ke yanki mafi girma da kuma muhimmanci a siyasar Jamus, North Rhine-Westphalia, wadanda ke ra'ayin tattaunawar ta samu bisa sharadin jagoransu Martrin Schulz, ya jajirce kan manufofin da suka danganci shige-da-ficen baki da na lafiya da kuma wadanda suka shafi ayyuka.