Afirka ta Kudu: Zuma a gidan kaso
July 8, 2021Wannan dai shi ne karon farko da wani tsohon shugaba a kasar ke fuskanatar zaman gidan kaso. A daren Larabar da ta gabata ne tsohon shugaban na Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya kai kansa ga jami'an tsaro, a wani mataki na fara zaman watanni 15 a gidan yari da kotu ta yanke masa. Kotun ta yanke masa hukuncin ne sakamakon kin mutunta gayyatar da ta yi masa zuwa bayar da bahasi, a kan bincikin sama da fadi da kudin al'umma da ake zargin gwamnatinsa.
Karin Bayani: Zawarcin wanda zai maye gurbin Jacob Zuma
Tuni gidan yari na Estcourt da ke yankinsa na Kwazulu Natal mai nisan kilomita 175, suka tabbatar da cewar Zuma ya na wajensu. Tun da fari dai Zuma mai shekaru 79 a duniya ya ki ya amsa wannan gayyata, abin da ya tilasta masa tafiya gidan kason. Dandazon da daruruwan magoya bayan tsohon shugaban Afirka ta Kudun suka yi a gidansa da ke mahaifarsa da nufin hana gurfanar da shi dai, bai yi wani tasiri ba. #b#
A tarihin kasar dai, wannan shi ne karon farko da tun kafin wannan lokacin, wani tsohon shugaban kasa ke zuwa gidan yari. To sai dai Zuma ya bayyana cewa ya gwammace zuwa gidan mazan maimakon ya gurfana a gaban kuliya, inda ya alakanta tuhumar da cewa bita da kullin siyasa kawai ake yi masa.
Karin Bayani: Zuma ya sha alwashin daukaka kara
Zuma ya jaddada cewa baya tsoron sake komawa gidan yari tun da a can baya ma ya taba yi. Wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudun da suka goyi bayan kin zuwansa kotun, na cike da bacin rai game da matakin kai shi gidan mazan. A nata bangaren jam'iyyarsa ta ANC ta ce ba za ta yi katsalandan a matakin shari'ar ba, a cewar mai magana da yawun jam'iyyar Pule MaBe. A ranar Litinin da ke tafe ne kotun tsarin mulki za ta yi wani zama domin nazarin bukatar Zuma ta janye zaman gidan kaso, bayan da ya shaidawa shugabannin gidan yarin cewa zaman gidan kson na da illa da lafiyarsa, kasancewar ba shi da isasshiyar lafiya.