Ja in ja tsakanin Zuma da jam'iyyar ANC
February 14, 2018Wannan mataki na jam'iyya mai mulki ta ANC a Afrika ta Kudu na zuwa ne 'yan sa'o'i kalilan bayan da 'yan sanda suka afka wa gidan iyalan Gupta 'yan asalin Indiya masu arziki a kasar ta Afirka ta Kudu da ake zargi da hannu a badakalar cin hanci da wawure dukiyar kasar saboda samun dama daga bangaren shugaban kasa. Kuma ana zarginsu ne da cin hanci kan harkokin makamashi da albarkatun mai da sauransu a Afirka ta Kudu, kuma hakan ya sake fito da karin matsin lamba da shugaban ke fiskanta na neman ya sauka daga mulki.
Shugaba Zuma dai ya bayyana cewa shugabannin jam'iyyarsa ba su ba shi sahihan dalilan da za su sanya ya sauka daga kan karagar mulkin kasar ba, kuma abin da aka yi na bukatar ya sauka daga mulki ba a yi masa adalci ba, inda a wata hira da aka yi da shi ya ce bai fahimci dalilin da suka bayar na neman ya sauka ba: "Ina bukatar ganin an bani bayanai kan abin da aka ce na yi, abin takaici babu wani da ya ce ga abin da na yi, muna bata lokaci wajen fadin cewa Zuma dole ya tafi ni na gaza fahimta mene ne dalili?"
Zuma dai ya yi wannan jawabi ne a tattaunawar da ya yi me tsawo da kafar yada labarai ta SABC adaidai lokacin da al'ummar kasar ke jiran sauraron ko zai sanar da ajiye mulki. To ko wane tsari jam'iyyar za ta bi wajen sauke shugaban? Jackson Mthembu shi ne bulaliyar majalisa a majalisar dokokin kasar ta Afirka ta Kudu inda yake cewa: "tsarin da a ke bi ne a kullum wajen zabin shugaban kasa, ba zamu yi amfani da sashin doka mai lamba 90 ba domin wannan sai baka da zabi sai a bawa mataimakakin shugaban kasa ya ja kujerar shugaban kasa ko wani mamba na majalisar ko kuwa kakakin majalisa, amma a wannan karo mun ce ne bara mu hanzarta mu zabi shugaban kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya bamu dama".
Babban ma'ajin jam'iyyar ta ANC ma dai Paul Mashatile ya fada wa manema labarai cewa jam'iyyarsu wacce ke da rinjaye a majalisa za ta tube Zuma a ranar Alhamis, za ta kuma zabi mataimakinsa Ramaphosa da sanyin safiyar Juma'a, kuma Mashatile ya ce ba su da lokaci na batawa sun kammala shiri sai aiwatarwa ya na mai cewa: "Yanzu zamu ci gaba kamar yadda bulaliyar majalisa ya fadi ne a kudirin da aka gabatar mu kada kuri'ar yankan kauna a majalisa a gobe Alhamis ta yadda za a cire Shugaba Zuma daga kujerar mulki a zabi mataimakinsa Ramaphosa a matsayin shugaban kasa yadda zai samu damar yin jawabi kan halin da kasa ke ciki kafin ranar Laraba 21 ga watan nan na Fabrairu ya gabatar da jawabi kan kasafin kudi."