1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An kashe jami'an tsaron Isra'ila uku a iyakar Jordan

September 8, 2024

Wani mahari ya halaka jami'an tsaron Isra'ila uku yayin da ya bude musu wuta a iyakar Jordan da Gabar Yamma da Kogin Jordan.

https://p.dw.com/p/4kPLc
Israel | Allenby Grenzübergang nach Jordanien
Hoto: Ahmad Gharabli/AFP/Getty Images

Sojojin Isra'ila sun ce an halaka jami'an tsaron kasar uku a ranar Lahadi a yayin da wani direban motar dakon kaya ya bude wuta kan shingen jami'an tsaro da ke iyakar Jordan da Gabar Yamma da Kogin Jordan da ke zama yankin Falasdinawa da Isra'ilar ta mamaye tun a shekarar 1967.

Karin bayani: Yakin Hamas da Isra'ila na kara ta'azzara

Wata majiyar tsaro a Jordan ta ce bayan harin Isra'ila ta dauki matakin sai baba ta gani na rufe mashigar da ke zama kofa daya tilo da ke sada al'ummar Falasdinu da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da sauran sassan duniya.

Karin bayani: Isra'ila ta kaddamar da mummunar farmaki a Jenin

A cewar rundunar sojin Isra'ilarmaharin da ya fito daga Jordan ya tunkari gadar Allenby cikin wata babbar mota, bayan isarsa shingen jam'an tsaro ne ya fito daga cikin motar sannan ya bude musu wuta.

Sai dai rundunar sojin ta ce an yi nasarar harbe maharin har lahira, sannan a daura guda ministan cikin gida na Jordan ya umurci da a gudanar da bincike kan aukuwar wannan lamari.