1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yakin Hamas da Isra'ila na kara ta'azzara

Abdoulaye Mamane Amadou
December 8, 2023

A daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke kara tsananta hare-hare ta kasa da sama a zirin Gaza, hukumomi a yankin sun ce Falasdinawa dubu 17 ne suka mutu tun bayan kaddamar da farmakin Isra'ila kan Hamas

https://p.dw.com/p/4ZuXv
Hoto: Ahmad Hasaballah/Getty Images

Watanni biyu bayan kaddamar da harin ramuwar gayya kan mayakan Hamas da Isra'ila ta yi, ana ci gaba da gwabza yaki a kwaryar Zirin Gaza, a yayin da a share daya dakarun Isra'ila ke tsananta luguden wuta a Khan Yunes.

Ma'aikatar harkokin lafiyar Falasdinu ta ce ya zuwa wannan Alhamis Falasinawa dubu 17 ne suka rasa rayukansu a fadan, a daidai lokacin da kudancin Zirin na Gaza ke cikin wani rudani na gaba kura baya siyaki a sakamakon kan nausawar da dakarun Isra'ila ke yi a yankin.

Hukumomi sun ce mutane da dama na tserewa daga yankin zuwa kan iyaka da Masar. Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta soki rashin cika alkawarin Isra'ila na kare fararen hula a kokarinta na kakkabe mayakan Hamas da wasu manyan kasashen duniya ciki har da Jamus da Amurka suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'dadda.

Ana sa ran nan ba da jimawa ba babban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya sake kira ga wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da shigar da kayan agaji.