Isra'ila ta kaddamar da mummunar farmaki a Jenin
August 29, 2024Harin na Jenin na kasancewa farmaki mafi muni a watannin da aka shafe ana yaki tsakanin Isra'ila da Hamas a zirin Gaza, tun bayan harin da mayakan Hamas suka kaddamar kan Isra'ilan a ranar 7 ga watan Oktoba.
Karin bayani: Hare-hare Isra'ila sun yi ajalin fararen hula a birnin Jenin
Mai magana da yawun sojin Isra'ila, Laftanal Kanal, Nadav Shoshani, ya ce sojojin Isra'ila sun shiga yankin Jenin da ke gabar yamma da kuma Tulkarem har ma da yankin Al-Faraa, da ya kasance sansanin 'yan gudun hijrar da ke arewacin Gabar Yamma a lokacin yakin Gabas ta Tsakiya a shekarar 1948.
Karin bayani: Dakarun Isra'ila sun janye daga Jenin
Hukumomin Falasdinu sun ce harin na Jenin ya halaka akalla mayakan Hamas guda goma, tare kuma da wasu mutanen guda hudu. Gwamnan Jenin Kamal Abu al-Rub, ya gabatar da jawabi a gidan radiyon Falasdinu inda ya ce dakarun Isra'ila sun yiwa birnin kawanya tare da dakile hanyoyin zuwa asibiti da kuma na shige da ficen birnin.