1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada firaministan rikon kwarya a Gabon

Abdullahi Tanko Bala
September 7, 2023

Jagororin juyin mulkin Gabon sun nada wani fitaccen mai adawa da hambararen shugaban kasar Ali Bongo a matsayin Firaministan rikon kwarya.

https://p.dw.com/p/4W5MD
Raymond Ndong Sima
Hoto: Scott Ngokila/Afrikimages Agency/IMAGO

Raymond Ndong Sima mai shekaru 68 ya taba rike mukamin firaminista a karkashin mulkin Bongo daga shekarar 2012 zuwa 2014

Daga baya ya zama mai kakkausar adawa da Bongo ya kuma yi takara da shi a zabbukan 2016 da 2023.

Sai dai bai tabuka abin a zo a gani ba a zaben baya bayan nan wanda sakamakon sa mai cike da rudani ya bai wa Bongo nasara wadda a karshe ta janyo juyin mulkin soji a kasar.

A waje guda wani mai shiga tsakani na kungiyar raya cigaban kasashen gabashin Afirka ya sanar da cewa gwamnatin mulkin sojin ta ce a shirye ta ke ta tsara jadawalin mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya.