1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dalilan sojoji na kifar da gwamnatin Ali Bongo

Muntaqa Ahiwa Abdoulaye Mamane
August 30, 2023

Sojojin kasar Gabon sun sanar da kifar da gwamnatin farar hula, sa'o'i kalilan bayan kammala zaben shugaban kasar da ya bai wa shugaba Ali Bongo mai ci nasara.

https://p.dw.com/p/4VkRo
Mutane na jinjina ga sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula a Gabon
Mutane na jinjina ga sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula a GabonHoto: Gaetan M-Antchouwet via REUTERS

A cikin jawabin da ya gabatar, guda daga cikin sojojin da ba a bayyana ko wane ne shi ba, ya ce sun soke zaben da hukumar zabe ta sanar da shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya yi nasara, da kundin tsarin mulki da majalisun dokokin kasar da ma sauran hukumomin gudanarwa a Gabon, inda ya ke cewa.

 "Kyakkyawar kasarmu Gabon ta jima a matsayin wadda aka sani da kasa ta zaman lafiya, amma a yanzu tana cikin rudani na mulki da siyasa da tattalin arziki gami da zamantakewa. Dole a yarda cewa zaben da aka yi a ranar 26 ga watan Agustan nan bai cika sharudan zama mai tsafta ba ko karbabbe ko ma wanda ya yi wa kowa adalci kamar yadda ‘yan Gabon ke zaton samu ba. Mulki da ake gudanarwa a kasar nan na ci gaba da lalata zamantakewar al'uma da ke kan shirin jefa kasa cikin rikice-rikice. A ranar 30.08.2023, a madadin al'umar kasar Gabon kuma a matsayin mu na masu tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyi na kasa, mun rusa gwamnati da majalisar dokokinta da kotun kundin tsarin mulki. Mun kawo karshen wannan gwamnati, saboda haka ma zaben da aka yi a ranar 26 da aka yi son zuciya a sakamakonsa, ya zama rusasshe."

An rufe iyakokin Gabon na sama da na kasa

Sojojin da suka kifar da gwamnatin Ali Bongon na Gabon sun kuma sanar da rufe iyaykokin kasar na sama da na kasa, kana sojojin sun sanar da wannan mataki da rushe-rushen da suka biyo baya, sun kuma bukaci kowa ya kwantar da hankulansu musamman ‘yan kasar wadanda ke waje. A yayin dai da aka ga juye-juyen mulki a wasu kasashen Afirka da sojojin ke cewa sun yi ne kan matsalolin tsaro, su sojojin Gabon da ke tsakiyar nahiyar sun ce sun kifar da gwamnatin ne a kan rashin kyawun zabe da al'uma ta jima da kokawa a kansa, kuma sun jaddada cewa sun yi hakan ne da nufin dawo da kasar bisa turbar gaskiya da amana, daga gwamnatin da gida daya ke mulki yau sama da shekaru 55.

Janar Brice Oligui Nguema jagoran juyin mulkin kasar Gabon tare da sojoji suna yi masa jinjina
Janar Brice Oligui Nguema jagoran juyin mulkin kasar Gabon tare da sojoji suna yi masa jinjinaHoto: Handout/Gabon 24/AFP

Karin Bayani: Ya babban zaben kasar zai kasance a Gabon?

Umar Bongo, mahaifin hambarerren shugaban kasar na yanzu wato Ali Bongo, ya mulki Gabon a tsawon shekaru 42 kafin mulki koma hannun dansa a shekarar 2009, bayan mutuwarsa. Gwamnatin Gabon din dai ta sanar da kafa dokar hana zirga-zirga a fadin kasar baya ga katse hanyoyin sadarwar Intanet da aka yi. Duk wani zabe da aka gudanar a kasar mai arzikin mai, na karewa ne da rigingimu tun a shekarar ta 1990 da ta koma tsarin jam'iyyu barkatai na siyasa.

Duniya na kallon abubuwan da ke faruwa a Gabon da idon basira

Kasar Faransa da ta yi wa Gabon mulkin mallaka dai ta ce tana bibiyar abubuwan da ke faruwa a kasar bayan tashi da wannan labari a yau. Firaminitar Faransar Elisabeth Borne ce ta sanar da hakan a wannan Laraba, jim kadan bayan sanarwar sojojin na Gabon.

Ana kallon Faransa da ke kasar farko da ta yi martini kan juyin mulki a matsayin wadda tasirin da ma kimarta ke raguwa matuka a nahiyar daga dai yawan juyin mulki da sojoji suka yi a shekarun nan. Yanzu dai hankali ya koma kan matakin da manyan kungiyoyi irin su AU ta Tarayyar Afirka da wasu na yankin tsakiyar Afirka za su dauka game da juyin mulki a kasar Gabon.