Gabon: Cece-kuce kan zaben Shugaba Bongo
September 29, 2016Talla
Kotun tsarin mulkin kasar Gabon ta tabbatar da zaben Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 27 ga watan Agusta 2016. Sai dai abokin hamayyarsa a zaben Jean Ping dama kasashen Turai sun nuna rashin gamsuwarsu da aikin kotun tsarin mulkin.