Ali Bongo na fuskantar kalubalen kasashen duniya
September 27, 2016Kotun tsarin mulkin kasar ta Gabon ta tabbatar da cewar shugaba Ali Bango ne ya lashe zaben da kashi 50,66% a yayin da abokin hamayyarsa Jean ping ya tashi da kashi 47,24 cikin dari. Sai dai tuni Jean Ping din ya nuna rashin amincewarsa da sakamakon aikin kotun tsarin mulkin kasar ta Gabon yana mai cewar kotun ba ta yi adalci ba.
''Ta hanyar daukar wannan mataki, kotun ta zabi ta kwace wa 'yan kasar Gabon 'yancin da kundin tsarin mulkin kasarsu ya ba su na zabar shugaban kasarsu domin al'ummar Gabon ba za ta taba fahimtar wanann sakamako ba."
Tawagar masu sa ido na kungiyar tarayyar Turai ta bakin jagoranta Mara Gabriel ta ce ba ta ji dadi ba da yadda kotun tsarin mulkin kasar ta Gabon ta gaza yin gyaran da yakamata kan kura-kuran da aka tafka a lokacin sake aikin kididdige sakamakon zaben. Musamman dangane da sakamakon zaben jihar Haut-Ogooue inda aka ce shugaba Ali bango samu kashi 95 cikin dari na kuri'un da aka kada a yankin da a nan ne madugun 'yan adawar kasar ta Gabon ya bukaci da a sake kirga kuri'un. Daga bangaransa ministan harakokin wajen Faransa Jean Marc Ayrault ya ce aikin da kotun ta yi ya janyo rudani. Ita ma dai kungiyar tarayyar Afirka ta bakin shugabanta Idriss Deby na Chadi sakamakon aikin da kotun tsarin mulkin ta yi na bukatar sake tatancewa. Shi ma babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon cewa ya yi kawai sun ga sakamakon aikin kotun tsarin mulkin ba tare da yin wani karin bayyani ba , sai dai ya bukaci mahukuntan kasar ta Gabon da su saki illahirin mutanen da suke tsare da su ba kan ka'ida ba.