Finidi ya zama sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya
April 29, 2024A cikin wata sanarwa da hukumar gudanarwar ta NFF ta fitar a Abuja, ta ce dukkan mambobin kwamitin sun amince da nadin Finidi George 'dan shekara 52 da zai jagoranci kungiyar ta Super Eagles.
Karin bayani: Najeriya ta sanar da makomar kocin Super Eagles
Da farko hukumar kwallon kafar Najeriya ta so ta nada mai horaswa daga kasashen ketare, amma ma'aikatar da ke kula da wasanni ta Najeriya ta nuna rashin amincewa sakamakon karancin kudi biyan Koci tare da neman a nada mai horaswa daga Najeriya. An fara ambato sunan Daniel Amokachi kafin a samu daidaito a kan Finidi George.
Karin bayani: Najeriya: Kalubalen da ke a gaban Super Eagles
Babban kalubalen da ke gaban sabon mai horas da kungiyar ta Super Eagles shi ne tabbatar da cewa Najeriya ta cancanci kai wa gasar cin kofin duniya FIFA 2026, musamman a wasannin share fagen shiga, inda Super Eagles za ta kalubalanci kasashen Arika ta Kudu da Jamhuriyar Benin a watan Yunin 2024.