1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NFF: Najeriya ba za ta kori kocinta ba

November 20, 2020

Najeriya ta nuna alamun ba za ta dakatar da kwantaragin Gernot Rohr mai horas da 'yan wasan kwallon kafa ta Super Eagles ba.

https://p.dw.com/p/3lcHk
Fußball WM 2018 Nigeria vs Argentinien Trainer
Hoto: Getty Images/AFP/G. Bouys

Rubutun da Ministan Harkokin Wasannin kasar Sunday Dare ya yi ne a Twitter na cewa yana  tababa kan kwarewar kocin biyo bayan gazawar Super Eagles ta lashe duk karawar da ta yi a wannan shekarar, ya haifar da jita-jitar cewa a wannan Jumma'ar hukumomin Najeriya za su sallami Gernot Rohr. 

To sai dai Shugaban Hukumar Kwallon Kafar kasar, Amaju Pinnick ya sanar a wannan Jumma'a cewa ko kodan ba za su dakatar da kocin ba, yana mai tunasar da masu yada jita-jitar cewa Gernot Rohr shi ne ya jagoranci Najeriya har ta samu damar shiga kofin duniya kuma ta zo na uku a gasar cin kofin Afirka. A bisa wannan Pinnick ya ce Najeriya za ta ba kocin na Super Eagles damar jan ragamar kasar zuwa kofin duniya da kofin CAF da za a yi shekara ta 2022.