NFF ta kori kocin Super Eagles
December 13, 2021Talla
Hukumar ta sanar da Augustine Eguavoen a matsayin kocin kungiyar Super Eagles na wucin gadi bayan da ta raba garo da Gernot Rohr. Tun a watan Augustan shekarar 2016 ne Rohr ke horas da 'yan wasan kungiyar, kuma shi ya jagoranci Najeriya har zuwa wasannin gasar cin kofin duniya a shekarar 2018. A daya hanun kuma ya kaita wasan kusa da na zagayen karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2019.
Sai dai kuma koci Rohr na shan suka kan rashin samun sakamako mai kyau a wasannin baya-bayan nan. Najeriya dai na cikin rukuni na D tare da kasashen Masar da Sudan da kuma Guinea-Bissau a gasar kwallon kafa ta Afirka da za ta gudana a Kamaru a farkon shekara ta 2022.