Zanga-zangar dalibai ta jawo damuwa a Nijar
April 11, 2017Dalibai biyu ne suka rasa rayukansu a wannan zanga-zangar yayin da dama suka jikata kuma aka cafke wasu daga cikinsu. Mounkaila Mamane Ibrahim mamba na kungiyar daliban Nijar ya ce "an binne dalibi daya yayin da gawar dayan kuma ke hannun jami'ai don gano musabbabin mutuwarsa."
Daliban na jami'ar birnin Yamai sun gudanar da zanga-zangar ne don nuna adawa kan mummunan halin rayuwa da kuma karatunsu ke ciki. Sannan kuma sun ce ba a ba su tallafin karatu na tsawon wani lokaci ba.
Su ma kungiyoyin iyayen dalibai sun nuna jimaminsu kan wannan lamari. Soulaymane Siratan da ke zama mataimakin shugaban kungiyar na kasa baki daya ya ce suna cikin bakin ciki saboda "batun ilimi ba ya tafiya yadda ya kamata, balle yaranmu su samu nasara a karshen shekara. Sannan ba mu ji dadin abin da ya faru tsakanin dalibai da jami'an tsaro ba."
Ministan da ke kula da ilimi mai zurfi na Nijar Ben Omar Mohamed ya yi alkawarin tattaunawa da wakilinmu na Yamai Mahaman kanta kan wannan batu. Sai dai har yanzu shuru kake ji.
Dama a ranar Litinin an samu irin wannan zanga-zanga a biranen Maradi da kuma Zinder.