1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan sanda sun haramta zanga-zanga a tsakiyar birnin Nairobi

July 18, 2024

Hukumomi sun ce sun gano bata gari na yunkurin shiga zanga-zangar domin tada tarzoma.

https://p.dw.com/p/4iTbm
Zanga-zanga a Kenya
Zanga-zanga a KenyaHoto: Daniel Irungu/EPA

'Yan sanda sun haramta zanga-zanga a tsakiyar birnin Nairobi fadar gwamnatin Kenya.

A wata sanarwa da mukaddashin shugaban 'yan sandan na kasar Douglas Kanja ya sanya wa hannu haramcin ya fito ne bayan rundunar ta ce akwai wasu bata gari da suka saje da masu zanga-zangar kuma suke neman tada hankali.

Sai dai masu fafutuka sun kirayi mutane su yi zanga-zangarsu a wata farfajiya da ke kusa da tsakiyar birnin duk da wannan gargadin na 'yan sanda.

Matasa da suka jagoranci zanga-zangar ta Kenya sun ci gaba da yinta duk da salwantar rayuka da aka samu.

Karin bayani:'Yan sanda na murkushe zanga-zanga a Kenya

Da farko an fara zanga-zangar ce don neman a janye dokar karin haraji sannan daga bisani suka sabonta bukatarsu tare da neman shugaba William Ruto ya sauka daga mukaminsa.