1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban rundunar ‘yan sandan Kenya ya yi murabus

Zainab Mohammed Abubakar
July 12, 2024

Tun bayan zanga-zangar adawa da shirin gwamnati na kara haraji ne dai, Shugaba Ruto ya sallami kusan dukkan ministocinsa.

https://p.dw.com/p/4iEIV
Japhet Koome Hoto: AP Photo/picture alliance

Shugaban rundunar ‘yan sandan Kenya ya yi murabus daga mukaminsa, sakamakon sukar da aka yi masa kan zanga-zangar kin jinin gwamnati da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama, a cewar fadar shugaban kasa, wanda shi ne babban  jami'i na baya bayan nan da guguwar zanga-zangar ta yi awon gaba da shi.

Shugaba William Ruto ya amince da murabus din Japhet Koome, babban sufeton 'yan sandan kasar, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.