Tsadar kudin makaranta na addabar dalibai a Najeriya
January 6, 2023A tsakanin kaso 150 zuwa 200% ne daliban jami'o'in tarrayar Najeriya suka fara biya, tun bayan kare yajin aiki na watanni takwas na malaman jami'o'in gwamnatin tarraya. Wannan matsalar na tada hankalin dalibai da suka fara zanga-zangogin neman soke karin da ke iya kaiwa ga sauya tsarin karatu na jami'o'in kasar.
Kama daga sashen arewacin kasar zuwa na kudancinta dai, daliban jami'o'i da dama sun fara zanga-zangogi don nuna adawa da sabon shirin da ke zaman barazana mai girma a tunani na dalibai, kamar yadda Kwamared Bashir Sulaiman da ke zaman ma'aiji na kungiyar daliban kasar reshen Arewa maso yammacin kasar ya bayyana.
Gaza kaiwa ga biyan bukatar jami'o'in daga bangaren gwamnatin tarayya ya kai ga karkatar da hankali zuwa ga sabon karin, wanda shugabannin jami'o'in ke fatan na iya kaiwa ga farfado da harkoki na karatu a jami'a. Ya zuwa yanzu dai, gwamnatin Najeriya na shirin kafa wani sabon banki da nufin bada lamuni ga daliban da nufin iya sauke nauyin da ta saba na karatu a kyauta. Shi ma Dr Abdulkadir Mohammed, babban jami'i na kungiyar malaman jami'o'i na kasar ASUU a jihar kano, ya ce babu amincewar malamai cikin sabon karin.
Adabo da karatu na jami'a a bangaren talakawa ko kuma kokari na inganta karatu dai, tun ba'a kai ko'ina ba, iyaye na kukan kasawa cikin kasar da ke tsakanin sauke nauyi na tura da kudade na karatun 'ya'yansu. Kabir Yusuf da ke daukar nauyin 'ya'ya har guda uku a daya cikin jami'o'in kasar, ya ce da kamar wuya a iya kaiwa ya zuwa ga sabon karin.
Najeriya na da jami'o'i kusan dari da ke zaman mallakin tarraya da jihohi, kuma tare da kaiwa zuwa iya samar da kudaden da ake da bukata ya zuwa ingantaccen ilimi.