Taron kolin kasar Indiya da kasashen Afirka
October 29, 2015A cikin sabon fata na samun sauyi da ma nishadi da annashuwa ne dai wakilan miliyan dubu daya da dari biyu da kusan hamsin na al'ummar Indiya ya kai ga hadewa da wakilan wasu dubu da dari biyu da kusan hamsin na nahiyar Afirka da nufin ginin daya mafi girma na kawance a duniya baki daya.
Da sunan gina sabon arziki mai launi na bula dai kasar ta Indiya na jagorantar kasashen Afirka 54 wajen gina abunda Firaminista Narendra Modi ya kira tattallin arziki da zamantakewa mai dorewa a tsakanin daya bisa uku na al'ummar duniya.
Kusan daukacin bangarorin biyu dai na kallon dama ta ginin tattalin arziki da ma samar da zamantakewa karkashin tsarin da ya kalli Indiyan sanar da damar bashi mai sauki na ruwa har na Dalar Amurka Miliyan dubu 10 nan da shekaru biyar masu zuwa, sannan kuma da agaji na Dala miliyan 600 domin raya kasashen na Afirka.
Tarihi da kalubale iri guda
Modin a cikin wani jawabin da ya koma lacca dai ya tabo tarihi da ma kalubale iri guda a matsayin babbar hujja ta hadewa wuri guda da nufin tinkarar makoma ta gaba a duniyar da a cewarsa ke cike da dama ga bangarorin biyu.
"Dangantaka ce da ta wuce dabara ta rayuwa ko kokarin gina tattalin arziki, an gina ta ne daga tunanin da muke dashi iri guda da kuma kokarinmu na taimakon juna. Cikin kasa da shekaru 10 ciniki a tsakaninmu ya ninka zuwa kusan Dalar Amurka Miliyan Dubu 70. Indiya ita ce daya daga cikin manyan kasashe na zuba jari a nahiyar Afirka. A yau kasashe 34 na Afirka na samun afuwar haraji na fito wajen kai kayansu a kasuwar Indiya. Makamashin Afirka na taimakawa wajen tafi da tattalin arziki na Indiaya. Sannan kuma albarkatunku ne ke taimaka mana wajen habaka kamfanoninmu da kuma tattalin arzikinku ta samar da kasuwa ga kayyayaki na Indiya."
A shekara ta 2008 ne dai aka kai ga samar da dama ta hadin gwiwa ta Indiya da kasashen Afirka a matsayin wata hanyar gine dangantaka tsakaninsu.
To sai dai kuma kasancewar kusan kowa a nahiyar a zauren taron dai na nuna alamar sako na irin tafiyar da ke gaba a tsakanin Afirka da ke neman dama ta mutunci a matakai daban-daban.
Ko bayan batun na kasuwa dai taron ya kuma koma dama ta siyasa ta duniya tare da sabo na kawancen jaddada neman sauyi a matakai daban-daban na siyasa ta duniya. Abun kuma da a cewar Robert Mugabe da ke zaman shugaban kungiyar Tarayyar Afirka ta sanya sabo na kawancen ke da muhimmanci a garesu.
"Tare mu 'yan Afirka da mu 'yan Indiya mun kai daya bisa uku na duniya baki daya. Tabbas daya bisa uku na al'ummar duniya mun ce mun ki da daukar mu kananan yara. Dole ne a mutunta dama ta daya bisa uku na duniya. Dole ne a mutunta daidaitonmu tsakanin kowa. Shi yasa muke cewar ya kamata a yi gyara a Majalisar Dinkin Duniya yadda za ta zamo dama ta samar da Majalisar Dinkin Duniya ta kasashe dai-dai."
Daya a cikin alamun nakin dai na zaman kasancewar shugaban kasar Sudan Omar Hassan El Bashir a cikin zauren taron duk da bukatar kotun duniya na neman kamashi. Sannan kuma da dagewar mafi yawa a cikin shugabanni 40 din da suka je birnin Delhi na tabbatar da kawo sauyi a yadda al'amura na duniya ke tafiya yanzu.
Sabbin dabarun tinkarar sauyin siyasa da tattalin arziki
Shugaba Muhammad Buhari dai na zaman jagoran Tarrayar Najeriya a zauren taron da kuma ya ce canji dole ko kafar katako in har ana neman kai karshen matsalolin da duniya take fuskanta yanzu.
"Cibiyoyin mulki na duniya sun tsufa, sannan suna nuna alamun gajiya kwarai, abun da ke bukatar sabbabi na dabaru domin tinkarar zahirin da ke akwai a sauyin na siyasa da tattali na arziki. Daga Arewa zuwa Kudu sannan daga Gabas zuwa Yamma kusan ko wace kasa a nahiyarmu na fuskantar talauci, da rashin aikin yi da karuwar yawa na matasa. Saboda haka dole ne Indiya da Afirka su gina sabon tsari da hadin kan da zai ba su damar tinkarar wadannan matsaloli."
Abun jira a gani dai na zaman sabbabi na dabarun da taron ke iya kaiwa ga fitarwa da nufin tinkarar kalubalen na talauci da ya shafi kusan biyu a cikin uku na daukacin al'ummar da ke cikin sabo na kawancen.