1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta rage tsadar rayuwa da tallafin Euro biliyan 65

September 4, 2022

A karkashin sabon tsarin gwamnati za ta bai wa tsofaffin ma'aikatan da ke karbar fansho Euro 300 kowanensu, yayin da hukumomi za su rarraba wa dalibai a kasar Euro 200. Za kuma a ci gaba da saukaka farashin sufuri.

https://p.dw.com/p/4GOsR
Deutschland Bundeskanzler Olaf Scholz
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Gwamnatin Jamus ta sanar a Lahadin nan da sabon tallafin kudade na Euro miliyan 65,000 da za ta yi amfani da su wajen saukaka wa al'ummomin kasar tsadar rayuwa. 

Sabon yunkurin na zuwa ne a daidai lokacin da Jamusawa suka fara fusata da tsadar rayuwar da suke fuskanta, inda wasunsu ke kurarin yi wa gwamnatin bore. Sai dai gwamnatin hadaka ta jam'iyyu uku a kasar ta bai wa 'yan kasar hakuri, ta kuma lashi takobin ci gaba da saukaka wa mutane harkar sufuri bayan karewar fitaccen tikitin sufuri na Euro tara da ya yi aiki na watanni uku. A yanzu gwamnatin Jamus din ta ce ta ware kudade sama da Euro miliyan dubu daya domin ci gaba da yin rangwame a farashin sufurin. Amma wasu na cewa farashin tikitin zai dara Euro tara da aka sayi tikiti a watannin baya.

Da yake magana kan kwan-gaba-kwan baya da Rasha ke yi wajen sayar wa Jamus da iskar gas, shugaban gwamnati Olaf Scholz ya ce ba abin damuwa ba ne, domin Jamus na da gas din zai wadaci mutanen kasar dumama dakunansu a yayin hunturun da ke tafe.