A cikin shirin za ku ji igiyar ruwa ta koro gawarwakin 'yan cirani zuwa gabar tekun Libiya. Akwai rahoton waiwaye game da yaki da cin hanci a Nijar da rahoto kan yadda aka yi biki Kirsimeti a karon farko a Saudiyya. Daga Najeriya akwai rahoto game da yadda hukumomi suka sanya wasu fursunoni karatun jami’a. Akwai shirin Labarin Wasanni da Noma da Raya Kasa.