1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar zargin juyin mulki ta dau sabon salo a Nijar

Mahaman Kanta/ YBAugust 19, 2016

Ana zargin wasu 'yan siyasa da soji da yunkuri na kifar da gwamnatin Shugaba Mahamadou Issoufou a ranar 18 ga watan Disambar bara. Yanzu dai bada belinsu ya gagara.

https://p.dw.com/p/1Jlnw
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou IssoufouHoto: Seyllou/AFP/Getty Images

Karo na biyu kenan da kotu a jamhuriyar Nijar ke watsi da neman beli na wasu jiga-jigai na siyasa da ma wasu sojoji da suka hadar da Janar Salifou Suleiman. Su kuwa 'yan siyasar sun fito ne daga jam'iyyar Modem Lumana ta Hama Amadou tsohon kakakin majalisa wanda ya yi takara daga gidan kaso a zaben shugaban kasar da ya gabata. Isuhu Isaka na daga cikin wadanda ake tsare da su daga cikin 'yan adawar, tsohon minista wanda kuma a yanzu ke zama dan majalisa a zaben da ya gabata.

Ana zargin wadannan mutane da yunkuri na kifar da gwamnatin Shugaba Mahamadou Issoufou a ranar 18 ga watan Disambar bara, ranar da ake cika shekaru 57 da Nijar ta zama jamhuriya.

Lauyoyin wadanda ake zargi dai na ganin kotu ba ta yi musu adalci ba, ganin sun gabatar da shedun da zai sa a basu belin.

Daga bangaren 'yan adawa da iyalan wadanda ke tsare kuwa sun nunar da cewa abin da kotu ta yi ba daidai ba ne, kuma hakan ya nunar da cewar za su bude sabon babi na adawa dan ganin sun sauya gwamnati a nan gaba.

Lauyoyin dai sun ce ba za su karaya ba inda za su nemi daukaka kara ta neman ganin an wa wadanda suke karewa sakin talala.

Niger Wahlkampf - Anhänger der Opposition
Dandazon 'yan adawa a NijarHoto: Getty Images/AFP/B. Hama