1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta yi kwanaki 100 da shiga Ukraine

June 3, 2022

Kafin Rasha ta mamaya Ukraine, mutane da yawa sun tsammaci cikin kwanaki uku an kammala komai. Sai dai zai kawo karshe a cewar Roman Goncharenko na sashen gabashin Turai a tashar DW.

https://p.dw.com/p/4CGvU
Yakin Ukraine | Charkiv I Hare-hare I Rasha
Yankuna da dama na Ukraine ne dai, hare-haren Rasha suka lalataHoto: Stringer/AA/picture alliance

Roman Goncharenko ya ce kwanaki 100 suna da yawa, ko ba su da yawa? Tambayar ita ce wane ne ya yi nasara, kuma wane ne ya yi rashin nasara? Idan aka ja layi kan mizanin yakin Ukraine dole a duba wasu matakai, idan aka zo ga sabuwar gwamnati. Kwanaki ne masu yawa, musamman a kasashen yamma. Da farko babu wanda ya yi tsammanin gwamnatin Kyiv za ta iya jure hare haren Rasha, ko da na kwana biyu ne zuwa uku. Watakila wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sa wasu kasashe ciki har da Jamus suka ja kafa wajen tallafa wa kasar Ukraine da makamai, abin da ake gani Jamus din ta yi kuskure. Wasu kasashen kuma musmaman Amirka da Birtaniya, suka rika jerin gwano wajen kai dauki. Ta haka suka taimaka, wajen kare murkushe Ukraine tun a farko fari. Shi ya sa darasin farko da za a iya cewa an koya tun bayan barkewar yakin shi ne, hanzarin kai taimakon makamai ya ceto rayuka.

Karin Bayani: Bikin cika shekaru 77 da Rasha ta yi nasara a yakin duniya na biyu

Idan muka tsaya ga misalin Jamus, lokacin da aka dauka tsakanin alkawarin taimakawa da hulunan kwano a watan Fabarairu da kuma sanarwar kwanan nan da gwamnatin ta yi na bayar da gudunmawar manyan makamai ga Ukraine na kakkabo jiragen sama, ya dauki tsawon watanni uku. Wannan ya yi tsawo matuka idan aka yi la'akari da tarihin Jamus, Berlin za ta iya yin abin da ya fi haka kuma sanarwar baya-bayan nan ta shugaban gwamnati ta karfafa gwiwa. To amma a daya bangaren idan aka dubi kwanaki 100 ba masu yawa ba ne, saboda yanzu ne ma aka fara yakin. Da farko Rasha ta fara ne da salon kai farmaki ba kakkautawa amma ba ta yi nasara ba, ta sauya dabara ta kassara karfin soja. Masu salon magana dai na cewa ba ka saurin cinye akushinka don gudun kada ka kware, wannan shi ne salon Ukraine na ci sannu a hankali, kuma wannan ya kawo mu ga darasi na biyu a wannan yaki.

Goncharenko Roman I DW
Goncharenko Roman na sashen gabashin Turai a tashar DW

Sai dai kash a zahirin gaskiya, Rasha ta dimauce kamar yadda ta sha farfaganda tsawon shekaru wanda mutane da dama ba su yi la'akari da ita ba. Wannan ko kadan bai dami Ukraine, ko Turai ko ma duniya baki daya ba. Shugaba Vladimir Putin ya fara yakin ne da manufar kwato yankunan da ya rasa, kuma ba shi da aniyar tsayawa. Barazanar Moscow ta yin amfani da makamin nukiliya, ba da wasa ta ke yi ba. Dole ne a yi dukkan abin da za a iya, domin dakatar da shi a yanzu saboda dukkan wani jinkiri na iya zama mai hadari. Ukraine na asarar sojoji da fararen hula da kuma yankunanta a kulli yaumin, kiyasi ya tabbatar da cewa dubban mutane sun mutu wannan babban abin bakin ciki ne aukuwar hakan a cikin kwanaki 100. Manufofin Rasha sun fara bayyana, a cikin gajere da matsakaicin lokaci tana so ta mamaye yankuna da dama na Ukraine da katse kasar daga hanyoyi na mashigar teku da kuma kakkabe dukkan wani abu da ya shafi Ukraine.

Karin Bayani: Matsayin kasashen Afirka a rikicin Rasha da Ukraine

Idan ta yi nasara sauran kasashe na gabashin Turai za ta burma su, su mika wuya ga Moscow ko kuma su fuskanci yaki mai tsanani. Yanzu an shiga mataki mafi hadari ana kazamin barin wuta a Donbass, idan ta yi nasara to za ta yi kokarin sake kwace Kyiv ta hambarar da gwamnati. Putin ba shi da niyyar tattaunawa, saboda yana jin cewa yana da karfin iko. Wannan yanayi da aka shiga yana da hadari saboda yakin ya fara zama jiki, sauran batutuwa sun fara mamaye kafofin yada labarai. An fara kosawa da yakin tun gabanin lokacin hutun bazara, bai kamata a yi sake ba. Zaman lafiya a Ukraine a yanzu ya zama almara, tana bukatar manyan makamai da kuma tsauraran takunkumi. Lokacin tattaunawa ta diflomasiyya zai zo ne kawai, bayan an dakatar da kutsen Rasha. Lallai ne a farga.