1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban 'yan Ukraine na bukatar taimako

March 7, 2022

Dubban 'yan gudun hijirar Ukraine da ke tserewa mamayar Rasha na cigaba da tsallaka kan iyakar Poland inda masu aikin agaji ke amsarsu.

https://p.dw.com/p/488dj
Russland-Ukraine Krieg Fliehende Menschen
Dubbai na tsere wa yakinHoto: Andriy Dubchak/AP/picture alliance

Yakin da Rasha ta afka wa Ukraine  ya haifar da kwararar 'yan gudun hijira mafi girma a nahiyar Turai da masana ke cewa, an dade ba a gani ba tun yakin duniya na biyu. A wannan Litinin magajin garin Lviv  Andriy Sadoviy da ke yammacin Ukraine ya ce, birnin ya wuce iya karfinsa na iya taimaka wa mutanen da Rasha ta tagaiyara da hare-haren da ta ke kai wa, inda ya bukaci agajin hukumomin kasa da kasa su taimaka.

Dubban mutane sun makale babu ruwa babu wutar lantarki a kudancin birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa, bayan yunkuri da aka yi har sau biyu na kwashe mutane ya ci tura saboda luguden wuta da Rasha ke yi a biranen Ukraine. A wajen birnin Kiev har yanzu ana ci gaba da harba makaman Atilare da makamai masu linzami wanda jami'an Ukraine suka ce haka lamarin yake a sauran sassan kasar.


Dubban yan gudun hijirar Ukraine din da ke tserewa mamayar Rasha na ci gaba da tsallakawa kan iyakar Poland inda masu aikin sa kai ke karbar su. Kawo yanzu 'yan gudun hijirar Ukraine da suka shiga cikin Poland sun haura mutum miliyan daya da dubu dari shida. Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa mutane da za su tsere daga Ukraine a sakamakon yakin, suna iya kai wa mutum miliyan hudu.
Ukraine ta yi watsi da tayin Moscow na bada damar wucewa, domin kai agaji bayan da ta kai hari kan wasu hanyoyi da jama'a ke kokarin ficewa domin tsira. Rashar dai ta yi tayin bai wa jama'a damar ficewa ne daga Kharkiv da Kyiv da Mariupol da kuma Sumy.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson a wannan Litinin, ya kare manufar Birtaniya na karbar 'yan gudun hijira da ke tserewa daga Rasha bayan da aka soki gwamnatinsa da cewa mutane 50 ne kacal ta bai wa vizar shiga cikin kasar.

Symbolbild Treffen | Putin Zelenskyy
Ukraine ta yi watsi da tayin Rasha na tallafa mata da agajiHoto: Russia/Ukraine Press Offices/AP/picture alliance


Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi sojojin Rasha da kisan fararen hula da gangan, bayan da wani hari ya hallaka wasu iyalai  da yayansu biyu da ke neman tserewa don samun mafaka. Sai dai kuma yayin da kasashen duniya suke cigaba da mayar da shugaban Rasha Vladimir Putin saniyar ware, daya daga cikin shugabanni kalilan da suke cigaba da bude kofar tattaunawa shi ne shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Ukraine-Krieg | Kiew morgens 25.02.22
Dubbai sun tsere daga gidajensu a UkraineHoto: GENYA SAVILOV/AFP


Yunkurin Macron na diflomasiyya domin hana aukuwar yakin ya ci tura sai dai bai karaya ba, shugabannin biyu sun tattauna sau hudu tun bayan da Rasha ta fara kai hari kan Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu sannan sun tattauna sau goma sha daya a tsawon watan da ya gabata.