1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Najeriya ta gaza cin moriyar sauyin tattalin arziki

November 18, 2024

Duk da ruwa da tsaki wajen cire tallafin man fetur a Najeriya, Asusun Lamuni na Duniya IMF ya ce sauye-sauyen arziki ba su yi tasiri ba. A cikin hasashen da ta yi, IMF ta ce kasar ba ta samu sakamakon da ake bukata

https://p.dw.com/p/4n7bK
Bunkasar al'umma ta kasa jawo wa Najeriya ci-gaba a fannin tattalin arziki
Bunkasar al'umma ta kasa jawo wa Najeriya ci-gaba a fannin tattalin arzikiHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

A wani abin da ke zama gagarumin koma baya ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ke fadin ta yi nisa a nasarorin sauyin tattalin arziki, Asusun Lamuni na Duniya IMF ya ce kasar ta gaza cimma moriyar jerin sauyin da ya kare da talauci a zuciyar miliyoyin 'yan kasar. A gefe daya, masu mulkin Najeriya na fadin cewar sun yi nasarar korar 'yan kamasho a tattalin arzikin kasar, kuma an dauki hanyar girma zuwa gaba. Sai dai a daya bangaren, Asusun Lamuni na duniya IMF ya ce har yanzu kasar na cikin duhu ga kokarin shawo kan rikicin tattalin arziki.

Karin bayani:Najeriya: Kokarin shawo kan matsalar tsadar rayuwa da kuncin jama'a  


Wani sabon rahoton IMF ya ce duk da jerin sauyin da gwamanatin kasar ta gabatar, Abuja ta zama kurar baya a tsakanin kasashen da ke Kudu da hamadar Sahara a fannin ci-gaba na tattalin arziki. IMF ya ce babu alamun aikin manufofin tattalin arzikin  da ya gaza kaiwa ga girman da ya kai kaso 3.6 da ke zaman hasashe na kasashen da ke kudancin na Sahara. Ya zuwa rabin shekarar 2024, Najeriya ta samu ci-gaban da bai wuci kaso 3.1 ba, abun da ya jefa kasar a baya a tsakanin kasashen da ke Kudu da sahara. IMF ta ce kasar gaza kaiwa ga cin moriyar jerin sauyin da ya azabtar da 'yan kasar, amma  ke shirin barin kasar cikin halin rudu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saba ma'amala da cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saba ma'amala da cibiyoyin hada-hadar kudi na duniyaHoto: Fayez Nureldine/AFP


Obasanjo ya caccaki manufofin Tinubu kan tattalin arziki


Kama daga kungiyar kodagon kasar ya zuwa jiga-jigan 'yan Najeriya dai,  zuciya ta yi baki bisa rudu na tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta. An ruwaito tsohon shugaban kasar Chief Olusegun Obasanjo, yana fadin cewar kasar ta rushe sakamakon kasawar manufofin tattalin arziki na gwamnatin Tinubu. Shi kuwa Daniel Bwala, da ke zaman  kakakin shugaban kasa, ya ce kafin karewar wa'adin farko na gwamnatin Najeriya, haske zai kai ga bayyana a gidajen 'yan kasar.

Karin bayani:  Najeriya na kokarin ceto darajar Naira

Najeriya ta dauki matakai da dama kan kudin Naira da ta fadi ba tare da farfado ba
Najeriya ta dauki matakai da dama kan kudin Naira da ta fadi ba tare da farfado baHoto: KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images

 Ko ma ina aka dosa don neman gyara dai, IMF ce ke zama a kan gaba a shawarwarin da suka sauya daukacin makomar kasar a kankanin lokaci. Amma Muttaqa Yusha’u da ke zaman shugaban gangamin waye kai a kungiyar kodago ta NLC ya ce sabon matsayin na kama da kokarin tserewa bayan tura daukacin kasar cikin babban rami. Abuja na da zabin mataki na gaba,  kasancewar gwamnatin na tsakanin burge masu jari hujja, da kuma tunkarar fushi na zuciyar talakawa  da ke ta kara karuwa a tsakanin al'ummar kasar a halin yanzu.