1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya: An rage albashin 'yan majalisa bisa radinsu

Uwais Abubakar Idris AH
July 19, 2024

Majalisar wakilan Najeriya ta amince da rage kashi 50 cikin 100 na albashin mambobinta na tsawon watani shida a kokari da rage matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta.

https://p.dw.com/p/4iWaj
Nigeria Politik l Senat
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

 Yan majalisar wakilan Najeriyar su 360 sun bi sahu na matakan tarba-tarba da gwamnatin Najeriyar ke dauka ne a kan matsanancin tsadar rayuwa da ke fusknatar alummar kasar saboda koma bayan tattalain arziki da faduwar darajara Naira, inda suka amince da ragewa kansu kashi 50 cikin 100 na albashin da suke karba a a matsayin tasu gudamawa, suna fatan wannan zai taimaka samar da sauki.

Nigeria Politik l Senat
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Ko da yake ‘yan majalisar suna ganin sun yi ta maza a kan daukan wannan mataki na rake kashi 50 na albashinsu da aka dade ana rufa rufa a kansa, sai dai bayanai sun nuna cewa ya zarta Naira milyan 1.9,  amma  ba' a nan take ba an dane budari a ka, domin alawus- alawus na kowane dan majalisa ya kaiu kimanin Naira milyan 29 kowane wata guda. Kama daga na kama gida zuwa motoci, tafiye- tafiye da sauran jin dadi,  wanda wannan kari bai shafa ba. Ibrahim Ismail Umar na cikin matasan Najeriyar da tsadar rayuwa ta sa suke yunkurin gudanar da zanga-zangar lumana a Najeriyar.

Nigeria | Bola Tinubu
Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Albashi dai na cikin nauyin da gwamnatin Najeriyar ke koke kan cewa yana lakume kudadde masu yawa da ya kamata a yi wa al'umma aiki kuma su gani a kasa. Shin wannan ragi da suka yi wane tasiri zai yi bisa la'akari da  halin da ake ciki. Duk da matakan da gwamnati ke dauka kama daga bada izinin shigo da kayan abinci daga kasashen waje ya zuwa ga rarraba kayan abincin tallafi musamman shinkafa da ma shirin dakatar da harajin Naira goma da ake sanyawa kayan zaki har yanzu hauhawan farashin kayayyaki na nan wacce ta zama tamkar ciwon ajali da baya jin   magani.