1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rikici a jam'iyyar APC

Uwais Abubakar Idris LMJ
March 5, 2020

A Najeriya an shiga rudani a jamiyya mai mulki ta APC biyo bayan daukaka kara da shugaban jamiyyar Adams Oshiomhole ya yi, kan dakatar da shi da wata kotu a Abuja ta yi

https://p.dw.com/p/3Yub3
Nigeria Oppositionspartei APC
Jam'iyya mai mulki a Najeriya na fama da rikicin cikin gidaHoto: DW/K. Gänsler

An dai ja layi tare da raba gari tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ta APC da ta dade tana fama da rigingimu na cikin gida da kamari da suka yi ya sanya wasu 'ya'yanta daukar mataki na shari'a, inda kotu ta bada umarnin dakatar da shugaban jamiyyar Adams Oshiomhole. Kwamared Mustapha Salihu shi ne mataimakin shugaban jamiyyar APC mai kula da yankin Arewa maso Gabas dai na daga cikin wandanda suka shigara da kara a kotun. To sai dai shugaban jam'iyyar ya ce bai yarda ba, inda tuni ma ya daukaka kara yana mai kalubalantar matakin a yanayi na duk wanda ya ce masa kule zai ce cas.

Ta dai yi zafi a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ta APC, domin bangarori biyu na nunawa juna dan yatsa a yanayi na ban yarda ba. A hannu guda kuma wasu 'ya'yan jam'iyyar irin su Yakubu Bulama akwai abin tsoro a daukacin al'amarin, yayin da suma masana ke ganin cewa jam'iyyyar na cikin hadari, tun da ta gaza yin sulhu a rikicin na cikin gida har ta kai ga daukar matakin shari'a. Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a kotun, a daidai lokacin da jam'iyyar ta APC ta afka cikin rikicin cikin gidan da za a iya daukar dogon lokaci ana tafkawa.