Babu tabbaci kan kan zaben Libiya
December 16, 2021
Mako guda kafin gudanar da zaben na Liiya da aka tsara yi ranar 24 ga wannan watan na Disamba, har yanzu hukumar zaben kasar ta gaza fitar da jerin sunayen 'yan takarar shugabancin kasar da ke ci gaba da dambaruwa gaban kotuna, don samun halaccin tsayawa takara, lamarin da ya sabawa dokar zaben kasar wacca ta tanadi cewa, makonni biyu kafin gudanar da zabe, za a fitar da sunayen 'yan takarar da za a ba su damar fara gudanar da yakin zabe.
To sai dai duk da hakan, jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a kasar ta Liiya, Stephanie Williams ta ce har yanzu ba ta fitar da ran gudanar da zaben a lokacin da aka tsara ba.
To sai dai kamar yadda Gamayyar kungiyoyi masu fafutukar girka dimukiraddiya a kasar ke fadi, gudanar da zabe kafin cimma matsaya kan amincewa da tsari da dokokin zaben tsakanin bangarorin da ke zaman 'yan marina a kasar tamkar yin kitso da kwarkwata ne.
Haka dai na zuwa lokacin da mayakan Janar Khalifa Haftar suka kai samame garin Sabha, tungar magoya bayan Saif al-Islam Gaddafi, wanda kotuna a kasar ta Libiya ke ta kwan gaba kwan baya wajen halaccin tsayawarsa takara. Dakarun na Haftar dai sun kwashe wani runbun makamai da motocin yaki na gwamnatin hadin kan kasa. Kana wasu mayakan sa kan sun kai farmaki kan majalisar zartarwa da ke birnin Tripoli, wasu mayakan kuma suka kai samamen kan hukumar zabe, sukai awun gaba da kayyakin zabe, lamarin da ke kara sanya rashin tabbas ga makomar zaben.