1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha ta musanta tattaunawar Putin da Trump a kan Ukraine

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 11, 2024

Jaridar The Washington Post ce ta wallafa cewa shugabannin biyu sun tattauna ta wayar tarho ranar Alhamis, har ma Putun din ya yi kira ga Trump da ya kaucewa rura wutar rikicin.

https://p.dw.com/p/4msg8
Sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Rasha Vladimir Putin
Hoto: ZDF

Rasha ta musanta rahoton da ke cewa shugaba Vladimir Putin ya tattauna da sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump ta wayar tarho kan yakinta da Ukraine, inda ta ce bata ga alamar shirya wannan tattaunawa daga kasashen yamma ba.

Karin bayani:Shugaba Putin na shirye domin tattaunawa da Trump

Mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov ya shaidawa manema labarai cewa labarin ba shi da tushe balle makama, yayin da shi kuma daraktan yada labran Donald Trump Steven Cheung ke cewa ba za su yi tsokaci kan duk wata tattauna da Mr Trump ya yi da shugabannin duniya ba kasancewar abin da ya shafe ne kai tsaye.

Karin bayani:Biden ya caccaki Donald Trump

Jaridar The Washington Post ce ta wallafa cewa shugabannin biyu sun tattauna da juna ta wayar tarho ranar Alhamis, har ma Putun din ya yi kira ga Trump da ya kaucewa rura wutar rikicin.