1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Shugaba Putin na shirye domin tattaunawa da Trump

November 8, 2024

Shugaban kasar Rasha na iya tattauanawa da zababben shugaban Amurka, bayan nasarar da ya samu a zaben da ya gabata. BAtun yakin Urkaine dai na daga cikin batutuwan da za su duba.

https://p.dw.com/p/4mntT
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha
Shugaba Vladimir Putin na kasar RashaHoto: Sergey Bobylev/Sputnik/REUTERS

Fadar mulki ta Kremlin a Rasha, ta ce a shirye Shugaba Vladimir Putin yake domin tattauna da zababben shugaban Amurka Donald Trump a game da Ukraine, sai dai kuma hakan ba zai sauya buri ko ma bukatunsa dangane ukraine din ba.

A jiya Alhamis ne dai Shugaba Putin din na Rasha, ya taya zababben shugaban na Amurka Mr. Donald Trump murnar lashe zabe, yana mai jinjina wa karfin zuciyarsa musamman ganin yunkuri da aka yi na halaka shi lokacin yakin neman zabe.

Yayin da aka nemi sanin ko shugaban na Rasha zai yi waya da Donald Trump, kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce babu wani abu mai karfi da ya danganci wannan a yanzu.

Sannan Dmitry Peskov ya ce zai yi wuri, a kawo batu ma na tattaunawa mai nasaba da alakar Rasha da Amurka a dai halin da ake ciki.