Lavrov na neman gyara mutuncin Rasha a Afirka
July 24, 2022Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya bude labulen ziyarar wasu kasashen Afirka a Lahadin nan da kasar Masar, inda ya fara yada zango a birnin Al-Kahira. Da isar sa Masar, Lavrov ya gana da Shugaba Abdel Fattah el-Sissi da sauran wasu manyan jami'an diflomasiyyar kasar.
Bayan kasar Masar, Lavrov, din zai wuce kasar Habasha da Yuganda da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kasashen da ake ganin ba su da kyakkyawar alaka da kasashen yamma a baya-bayan nan.
Galibin kasashen Afirka dai na dari-darin nuna goyon bayansu ga Rasha ko kuma kasashen yamma a rikicin Ukraine. To amma duk da haka rikicin ya yi wa tattalin arzikinsu mummunan illa, inda Afirkan ke dandana tashin farashin fetur da kuma tsaar kayan abincin da rikicin na Ukraine ya sabbaba.