Putin: Mun fi Amirka karfin makaman nukiliya
March 13, 2024Talla
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya jinjina wa kasar kan karfin makamin nukiliya da take da shi, yana mai gargadin cewa Rasha a shirye take ta fara amfani da wadannan makamai madamar aka taba mutuncin kasarsa.
''Mun shirya amfani da makamin nukiliya kuma makamanmu sun fi karfin na manyan kasashen duniya. Namu da na Amirka ne kawai suke daidai. Kuma mu mun yi nisa ma a inganta namu makaman masu guba a nan gida.'' in ji Shugaba Putin cikin wata hira ta musamman da aka yi da shi a kafar yada labaran Rasha
Kalaman na Shugaba Putin din na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da dakarun Ukraine suka kai wa matatun fetur na Moscow wani mummunan hari, masu sharhi kuma na ganin hakan ne ya sanya shi barazanar fara amfani da makaman nanukiliya.