Nijar na yunkurin gurfanar da Hama Amadou
August 26, 2014
Wani dan majalisar dokoki mamba a kwamitin gudanarwa na majalisar dokokin kasar, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa da misalin karfe uku (3) na yamma ne wasikar gwamnatin ta iso hannun kwamitin gudanarwar majalisar, a daidai loakcin da shugaban majalisar dokokin ke wata ganawa da su, domin bayyan aniyarsa ta shigar da kara a gaban kotun tsarin milki, domin kalubalantar aniyar gwamnati ta gurfanar da shi a gaban kuliya ba tare da cire masa rigar kariya ba.
Jim kada, bayan samun wannan wasika dai shugaban majalisar dokokin kasar ta Nijar ya ficce daga cikin majalisar zuwa babbar cibiyar jam'iyyarsa ta kasa, a yayin da a shari daya hukumomi suka jibge tarin jami'an tsaro a cikin motoci a gaban majalisar dokoki.
Daruruwan magoya bayansa sun yi cincirindo suna ambatan munanan kalamai ga gwamnati da kuma na nuna goyan bayansu ga gwanin nasu inda harma matan jam'iyyar tasa su ka sha alwashin ta ko wani hali hana gwamnatin cimma wanann buri nata na kama Hama Amadoun.
Illahirin kusoshin jam'iyyar ta Lumana Afrika dai sun hallara a cibiyar jam'iyyar ta kasa inda su ke shirin gudanar da wani taron nazarin hanyoyin tinkarar matakin neman kama shugaban jamiyyar tasu. Sai dai ko ma me ake ciki tuni kwamitin gudanarwa majalisar dokokin, wanda dama ke kunshe da yan majority ne kawai tun bayan da 'yan adawa su ka fice daga cikinsa, ya tsaida ranar
laraba (27.08.2014) a matsayin ranar da zai yi nazarin wasikar gwamnatin domin yanke shawarar mika Hama Aamdoun ko kuma aksasin haka
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Pinado Abdu Waba