Nijar na sayar wa manoma da taki a farashi mai sauki
August 13, 2024
Takin da gwamnatin Nijar ta samar na daga cikin tsarin da aka yi na tallafa wa kananan manoma da ke noman shinkafa da sauransu a karkashin kungiyar manoman shinkafa da ake kira Cooperative. Gwamnan birnin Yamai Birgediya Janar Assoumane Abdou Harouna tare da darektar jiha a ma'aikatar kula da harkokin noma da kiwo ne suka mika taki kimanin Ton 100 -100 ga gundumomi biyu na birninYamai da ake da masu noman shinkafa.
Karin bayani:Bunkasar kasuwancin albasa a Jamhuriyar Nijar
Gwamnan Yamai Janar Assoumane ya yi tsakaci kan wannan tsari, inda ya ce: " Mun karbi Ton 200 na takin zamani a hakumance wanda gwamnati ta saka tallafi a cikinsa domin sayarw gaa kananan manoma, masu karamin karfi sosai kuma a ba su a kyauta. Wadannan Ton 200, an raba su ga gunduma ta hudu da ta biyar na Yamai inda ake noman shinkafa a bakin kogin Isa. Karamin manomi zai sayi takin a jaka biyar, alhali a kasuwa ana sayar da shi a jaka 28, kuma mutun daya na iya samun bahu hudu na taki, wasu kuma da ke da karamin karfi sosai, an ware Ton 40 da za a ba su a kyauta.”
Karin bayani:Nijar ta ciyo bashin kudi daga Chaina
Babbar Darektar jihar Yamai a ma'aikatar da ke kula da harkokin noma da kiwo ta ce burin da aka sa a gaba shi ne ganin manoma sun samu amfani mai yawa ta yadda za su ciyar da kansu har su kai kasuwanni don sayarwa. Saboda haka ne shugaban Cooperative Saga da ke a matsayin uwar kungiya ta masu noman shinkafa Soumana Djibo ya ce sun ji dadin wannan tsari:
A birnin Yamai, sanin kowa ne cewar a yankunan da ke makwabtaka da kogin Isa ne ake noman shinkafa a kowace shekara. Sai dai duk da kuzarin da suke da shi, amma rashin karfin sayan takin zamani na hana manoma rawar gaban hantsi, kuma a cewar Ibrahim Moro wani manomi da ya ce shi ma an dauki sunansa daga cikin wadanda za su samu tallafin takin zamani, akwai manoma da dama da suke bukatar wannan tallafi daga gwammnati. Sai dai 'yan kungiyoyin fararan hula irin su Oumarou Souley da ke shugabantar kungiyar FCS ta masu kare hakin jama'a sun yi hannunka mai sanda na ganin an kawar dai son kai ko nuna bambamci wajen bada wannnan tallafi.
Karin bayani: Nijar: Sulhu tsakanin manoma da makiyaya
Yankuna da dama na kasar Nijar na noman shinkafa, duk da matsala iri daya da kananan manoma ke fuskanta wadda ita ce na rashin halin sayen takin zamani da zai ishi shinkafar da suke nomawa. Ana ganin cewar idan gwamnati ta fadada tallafin a ko'ina a fadin kasar ta Nijar, to za a gani a kasa a fannin samun cimaka, wanda hakan zai taimaka wajen magance matsalar karancin abinci a kasar.