1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar ta ciyo bashin kudi daga Chaina

Gazali Abdou Tasawa ZMA
April 15, 2024

Gwamnatin Nijar ta sanar da ciyo bashin kudi daga kamfanin main Chaina na CNPC ta hanyar jingina mata man fetur da Nijar din za ta hako a tsawon shekara daya.

https://p.dw.com/p/4en2a
Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Gwamnatin mulkin sojan ta ce ta dauki wannan mataki ne domin fuskantar wasu matsaloli kamar na tsaro da ke addabar kasar da kuma kaddamar da wasu ayyukan na ci gaban kasa da al'umma. Sai dai kuma tuni mataki ya soma haddasa zazzafar mahawara a kasar kan dacewar ciyo bashin musaman ta la'akari da yadda gwamnatin ta soki tsohuwar gwamnatin da shake kasar da bashin da ya wuce kima.

Karin banayi: 'Yan Nijar sun yi zanga-zanga neman ficewar sojojin Amurka

Kudi tsaba miliyan 400 na Dalar Amirka kwatankwacin CFA miliyan dubu 220 da ‘yan kai ne gwamnatin mulkin sojan kasar ta Nijar ta karba bashi a hannun kamfanin man fetur din gwamnatin Chaina na CNPC wanda ke mallakar kaso 76 cikin dari na ganga dubu 90 da Nijar za ta hako a yini a yayin da Nijar din ke da kaso 24 cikin dari.

A karkashin wannan yarjejeniya, Nijar, za ta dinga biyan bashin kudin nata kai tsaye ga kasar ta Chaina da man nata a tsawon shekara daya tare da biyan kudin ruwan kaso bakwai cikin dari. Kuma firaministan kasar Malam Ali lamine Zeine ya bayyana wasu daga cikin hanyoyin da suke son saka wadannan kudaden bashi da gwamnatinsu ta karbo.

Karin bayani: Ingantuwar dangantakar Rasha da Nijar

 "Za mu yi amfani da wadannan kudade ta hanyar aiwatar da bukatu mafi muhimmanci ga kasa, Da farko za mu saka su a fannin karfafa matakan tsaro a kasa ta hanyar sayan makamai da za mu tsare kasarmu da iyakokinta. Za mu bunkasa harkokin noma da samar da kamfanonin sarrafa kayan gona, zamu inganta harkokin kiwon lafiyar al'ummarmu, kana za mu yi kokarin biyan wani kaso na basussukan kasa da kasa da ake bin kasar musamman a sakamakon takunkumin da aka saka mata, kana za mu biya basussukan da ‘yan kasuwa da ‘yan kwangila na cikin gida suke bin gwamnati".

Tuni dai wasu kungiyoyin da ke goyan bayan gwamnatin mulkin sojan suka soma bayyana gamsuwarsu da matakin daukar wannan bashi wanda suka ce zai taimaka ga rage jerin matsalolin da kasar ta shiga musamman a sakamakon takunkuman da aka saka mata bayan juyin mulki.

Karin bayani: Masu adawa da kawance kasashen Sahel

To sai dai wasu masu adawa da mulkin sojan Nijar na ganin rashin dacewar daukar wannan bashin kudi, Malam Mahamadou Abdoulkader Maidalili daya daga cikin masu adawar zargin sojojin da ke mulkin ya yi da neman kitsa cuwa-cuwa a cikin lamarin.

Yanzu dai ‘yan kasa sun zura ido su ga ko bashin kudin da gwamnatin mulkin sojan ta ciwo wa Nijar zai taimaka ga ci gaban kasa da inganta rayuwar al'umma ko kuma za ta ci gaba da kasancewa gidan jiya noma goje kamar yadda ta kasance a karkashin mulkin farar hular inda aka kwashe shekaru ana cewa talaka ya gafara ga sa amma har kawo yanzu ba ga ko da kaho ba.