Nijar na murnar cika shekaru 62 da samun 'yancin kai
August 3, 2022Batun hadin kai ko na zamantakewa tsakanin 'yan kasa a Nijar, batu ne da magabata musamman ma tun a lokacin mulkin soja na marigayi Seyni Kountche, aka kafa babbar dan 'ba' ta hadin kai tsakanin kabilu inda ake tura ma'aikacin gwamnati dan wannan kabila zuwa wani yanki da ba na kabilarsa ba wanda sannu a hankali ta sanya aka samu cudanyar juna tun shekaru da dama da suka gabata.
Hon. Kalla Moutari dan majalisar dokoki ne kuma tsohon ministan tsaro a kasar ta Nijar cewa ya yi Nijar babu matsalar hadin kan yan kasar. Ko shi ma a nashi bangare Alhaji Doudou Rahama dan siyasa na bangaran adawa, cewa ya yi shi dai batun hadin kan 'yan kasa a Nijar daga bangaren 'yan takarda ne da 'yan siyasa yake a matsayin cikas amma ba ga talaka ba.
Sau tari dai 'yan siyasa ne ake zargi da haddasa cikas na raba kanun 'yan kasa bisa dalillai na son kai irin nasu. Kuma da yake magana kan wannan batu, Soumaila Amadou shugaban jam'iyyar PNUD Awaiwaya, ya ce magabata na farko sun yi iyakar kokarinsu na kafa dan 'ba' ta hadin kan 'yan kasa da samar da kyaukyawar zamantakewa, amma kuma daga bisani bakar siyasa da ake yi ta yaudara ta tabarbara komai.
Abun jira a gani dai shi ne ta yadda magabata na siyasa za su yi kokarin cire duk wani son kai su yi amfani da dokokin kasa ta yadda duk wani dan kasa zai ji shi ba tare da ana nuna wata wariya ko kyama ta dilillai na siyasa ba.