Sabon taken kasa a Jamhuriyar Nijar
June 21, 2023Gwamnatin Jamhuriyar Nijar din dai ta tsara sabon taken ne, domin maye gurbin wanda ta gado tun daga Turawan mulkin mallaka na Faransa shekaru 62 da suka gabata da ta ce ya saba wa tafiyar kasar ta wannan zamani. Kwamitin rubuta sabon taken na Nijar mai kunshe da mambobi 12, ya kwashe shekaru hudu yana aikinsa da nufin maye gurbin taken kasar na yanzu mai suna "La Nigérienne". Ba ya ga batun sanin kalaman da ya kunsa da ma ba shi suna, majalisar dokokin ta Nijar za kuma ta yi nazarin salon kidan da aka yi masa gabanin muhawarar da za su tafka su kuma kada kuri'a tare da yi wa kudirin farko na kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin a samu damar kaddamar da shi a hakumance. Majalisar dokokin ta Nijar dai ta lakabawa sabon taken kasar sunan "Au nom de la patrie" wanda ke da tsayin minti daya da dakika 43.