Narendra Modi sabon babi ga Indiya
May 16, 2014Ƙasar Indiya ta zaɓi sabuwar majalisar dokoki, inda masu kaɗa ƙuri'a suka ja kunnen jam'iyyar Congress Party da ke jan ragamar mulki bayan sun zaɓi jam'iyyar adawa ta BJP ƙarƙashin jagorancin Narendra Modi, wanda ya alƙawarta kawo canji.
A lokacin da bayyana gaban magoya bayansa bayan lashe zaɓen Narendra Modi cewa "ranaku masu kyau, ranaku masu kyau sannan mutane na amsa wa da cewa suna zuwa ba da daɗewa ba, suna zuwa ba da daɗewa ba. Wannan tafiya ce daga wuya zuwa daɗi. Al'umma za ta canja makomar Indiya."
Narendra Modi da jam'iyyarsa ta BJP dai ta samu gaggarumar nasara a zaɓen 'yan majalisar dokokin ta ƙasar Indiya. To sai dai mutumin da ake wa kallon wanda zai buɗe sabon babi ga Indiya, yana da wani tabo na tarihi da ka iya zame masa alaƙaƙai. Domin ana zarginsa a matsayin Firimiyan jihar Gujarat ya ƙi ɗaukar matakan hana 'yan kishin ƙasa 'yan Hindu kashe ɗaruruwan Musulmi a wani tashin hankali da ya auku a jiharsa ta Gujarat a shekarar 2002.
Dan ra'ayin kishin kasa na Hindu
Modi wanda ya fito daga wani gida na masu matsakaicin ƙarfi ya yi karatun fannin kimiyyar siyasa a jami'ar Gujarat kuma ya shafe shekaru masu yawa yana wa ƙungiyar 'yan kishin ƙasa ta 'yan Hindu wato RSS aiki kafin ya koma jam'iyyar ra'ayin riƙau ta 'yan Hindu wato BJP.
Daga ƙasa ya a iza sauraron wannan rahoto
Mawallafa: Srinivas Mazumdaru / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane